Sheikh Mansur Sokoto: Ma'anar Batanci ga Ma'aiki SAW da Hukuncinsa a Musulunci
- Babban malamin addinin Musulunci, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, ya fitar da fayyace matsayar addinin Islama game da batanci ga Fiyayyen halitta
- Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya bayyana abin da ake nufi da 'batanci ga Annabi Muhammad SAW da kuma hukuncin da aka tanada a kan masu kalaman
- Amma ya bayyana cewa duk da hukuncin da aka tanada, hukumomin da shari'a ce ne ke da alhakin zartar da wannan hukunci ba tare da bata lokaci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – A yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan zarge-zargen furta kalaman ɓatanci a Najeriya, malamin addinin Musulunci, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya yi cikakken bayani kan abin da ake nufi da batanci.
Ana samun wasu tsageru a Najeriya, Musulmai ko mabiya wasu addinan na furta kalaman batanci ga Annabi Muhammd SAW, lamarin da ke tunzura jama'a da jawo tashin hankali.

Kara karanta wannan
Hadimin Abba ya nanata zargin da ake yi wa Abdusalam Gwarzo na yin kwana da N308m

Source: Facebook
A hira da ya yi da BBC Hausa, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, ya yi bayani kan ma'anar laifin a Musulunci, nau'ikansa da kuma yadda shari'a ta tanadi a bi wajen hukunta wanda aka tabbatar da aikata shi.
Menene batanci ga Annabi?
Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, wanda ƙwararre ne a fannin Hadisi a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ya bayyana cewa kalaman ɓatanci su ne duk wani zagi, izgili, habaici ko kalaman da ke tauye daraja da mutuncin Annabi Muhammad (SAW).
Ya ce ba wai zagi kai tsaye kaɗai ake ɗauka a matsayin ɓatanci ba, domin duk wata magana da al'umma ta fahimta a matsayin cin mutuncin Manzon Allah ma tana shiga cikin wannan rukuni.
Farfesa Mansur ya ce fitaccen malamin Musulunci Sheikh Alƙadi Iyadh ya lissafo abubuwa kusan 20 da za su iya shiga cikin kalaman ɓatanci idan aka aikata su ga Annabi Muhammad (SAW).

Source: Facebook
A cewarsa, daga cikin su akwai zagi kai tsaye, aibanta halittarsa, cin mutuncin asalinsa ko danginsa, yin suka ga addininsa ko ɗabi'unsa, la'antarsa, yi masa mummunar addu'a ko jingina masa abin da bai dace da matsayinsa ba.
Sai dai Farfesan ya yi nuni da cewa a wasu lokuta ana samun ruɗani wajen fahimtar maganganun mutane, lamarin da kan sa a karkatar da abin da mutum ya faɗa a ɗauke shi a matsayin ɓatanci ba tare da cikakken tantancewa ba.
Hukuncin ɓatanci ga Annabi a shari'a
Dangane da hukuncin wanda aka tabbatar ya aikata ɓatanci, Farfesa Mansur ya ce malamai sun yi ijma'i cewa zagin Allah ko Manzon Allah babban laifi ne a Musulunci.
Ya bayyana cewa a tsarin shari'ar Musulunci, hukuncin da aka tanada ga wanda aka tabbatar da yin irin wannan laifi shi ne hukuncin kisa, yana mai cewa wannan hukunci yana ƙarƙashin ikon hukuma da kotun shari'a.
Ya kuma ce idan wanda aka samu da laifin ba Musulmi ba ne, za a ba shi damar musulunta, yayin da idan Musulmi ne za a umarce shi da ya tuba.
Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya ce:
"Allah ya shelanta cewa duk abin da ka yi idan ka roƙe shi zai yafe maka, amma tun da manzon Allah ba ya raye, al'umma ba za su iya yafe masa ba.
Sai dai ya jaddada cewa aiwatar da hukunci ba hakkin jama'a ba ne, domin yana gudana ne ta hanyar shari'a bayan an tabbatar da laifi da hujjoji. Wannan, in ji shi, shi ne tsarin da malamai suka bayyana a cikin manyan littattafan fikihun Musulunci.
Malami a masallacin Annabi ya rasu
A baya, kun samu labarin cewa musulmai a fadin duniya sun yi alhini bayan labarin rasuwar babban malamin addinin Musulunci a masallacin Annabi Muhammad (SAW) da ke Madinah a kasar Saudiyya.
Musulmi a faɗin duniya na alhinin rasuwar fitaccen malamin, Sheikh Dr. Rabi’ ibn Hadi al-Madkhali tare da addu'o'in Allah Ya gafarta masa, Ya kuma karbi ayyukansa na gari da ya aikata a rayuwarsa.
Hukumar kula da Harami ta tabbatar da rasuwar malamin, tana mai mika ta'aziyya ga iyalansa, dalibansa da dukkanin musulman da suka amfana da karatunsa da jagorancinsa a duniyar musulunci gaba daya.
Asali: Legit.ng

