"Ni ba Ungulu ba ne:" Ganduje Ya Yi Martani ga Zargin zai Hade da Kwankwaso

"Ni ba Ungulu ba ne:" Ganduje Ya Yi Martani ga Zargin zai Hade da Kwankwaso

  • Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi martani ga jita-jita da ta fara karfi cewa yana shirin rabuwa da jam'iyya mai mulki
  • Rahotanni daga jihar Kano sun yi zargin cewa akwai alamu masu karfi na cewa Ganduje zai iya hade wa da tsohon mai gidansa, Rabiu'u Musa Kwankwaso
  • Wannan batu ya jawo cece-kuce musamman a tsakanin magoya bayan APC da suka bar Kwankwasiyya, lamarin da ya jawo martanin Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sake jaddada cewa yana nan daram a jam'iyyar mai mulki.

Ganduje, wanda tsohon gwamnan APC ne ya ara da cewa duk ɗan siyasar da ke yawan sauya sheƙa daga wannan jam'iyya zuwa wata ba don komai ba ne sai wata buƙata ta siyasa ko son zuciya ba ne.

Kara karanta wannan

Bayan shan wuta, mayakin ISWAP na kan kogi ya mika wuya ga jami'an sojoji

Ganduje ya ce ba ba abin da zai kai shi NDC
Tsofaffin gwamnonin jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Hon Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya bayyana haka ne ta cikin sanarwar da hadiminsa, Kwamred Muhammad Lawan Garba ya fitar, kuma Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ganduje ya magantu kan hadewa da Kwankwaso

A cikin sanarwar da Abubakar Aminu Ibrahim ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ganduje ya bayyana rashin jin dadi a kan yadda wasu ke saka fastoci suna ikirarin cewa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar NDC.

A cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano kuma tsohon shugaban ma'aikatansa, Kwamared Muhammad Garba, ya fitar, Ganduje ya bayyana fastocin a matsayin ƙarya, yaudara da kuma wani shiri na siyasa da aka tsara domin yaudarar jama'a.

Sanarwar ta ce manufar yaɗa irin waɗannan bayanai ita ce rikita magoya bayan APC da kuma haifar da cece-kuce marasa amfani a fagen siyasa.

Sanarwar ta bayyana cewa Ganduje ya kasance mai tsayawa kan akidarsa ta siyasa, kuma bai taɓa yin tunanin barin APC ba, jam'iyyar da ya yi wa hidima har ya zama shugabanta na ƙasa.

Kara karanta wannan

Soke rajistar NDC: IPAC ta yi zargin ana shirin birne dimokuradiyya a Najeriya

Ba zan koma NDC ba - Ganduje

Ya ce ikirarin cewa ya koma NDC ba gaskiya ba ne, kuma babu wani dalili na siyasa ko na hankali da zai sa a gaskata irin wannan batu.

Ganduje ya ce mai yawan sauya sheka dan son zuciya ne
Tsohon shugaban AOC na kasa Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

A cewarsa, APC ita ce jam'iyya mafi girma kuma mafi ƙarfi a Najeriya, wadda ke ci gaba da samun karɓuwa a faɗin ƙasar nan tare da ƙarfafa matsayinta ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar ta zargi wasu masu tayar da fitina a siyasa da ƙirƙira da yaɗa fastocin domin bata sunan Ganduje da kuma haifar da fargaba a cikin jam'iyyar APC.

Ganduje ya ce an gano mutanen da ke da hannu wajen ƙirƙira da yaɗa fastocin bogin, yana mai gargaɗin cewa idan ba su janye su tare da daina yaɗa su ba, za a ɗauki matakin shari'a a kansu.

Ya kuma buƙaci 'yann APC, magoya bayanta da sauran al'umma su yi watsi da fastocin gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa ba sa wakiltar matsayinsa ko shirinsa na siyasa.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya nanata zargin da ake yi wa Abdusalam Gwarzo na yin kwana da N308m

Martanin Ganduje ga Kwankwaso

A wani labarin kun ji cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya tuna yadda ya taimaka wa madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Kwankwaso tun farko kafin ya kai ga zama mataimakinsa sau biyu a Kano.

Ya dauko wannan tarihi ne a matsayin martani ga kalaman Kwankwaso, wanda ya kira Ganduje da yaronsa na siyasa, inda ya kara da bayyana cewa uba na iya rainon dansa kuma daga baya ya fi shi daukaka.

A cikin sanarwar da ya fitar, Ganduje ya ce siyasa tana ginuwa ne a kan dangantaka, goyon baya, jajircewa da kuma jagoranci, yana mai cewa babu wani dan siyasa da zai kai matsayi ba tare da taimakon wasu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng