Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Amince a Dauki Ma'aikata 300 a Hukumar Bogi da Ake Cece Kuce
- Fadar shugaban kasa ta fito ta bayyana cewa ba ta san da hukumar PFIPC ba wadda Adeniyi Adeyemi ke ikirarin jagoranta
- Ta bayyana shi a matsayin dan damfara, inda ta nuna cewa ya yaudari babban bankin Najeriya (CBN) wajen bude asusun banki
- Sai dai, wasika da aka gani, ta nuna cewa gwamnatin tarayya ta amince a dauki ma'aikata har guda 300 a hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ba wa hukumar nan mai cike da ce-ce-ku-ce, wato hukumartallafin kasashen waje ta fadar shugaban kasa (PFIPC), damar daukar ma'aikata.
Gwamnatin tarayya ta ba hukumar PFIPC damar daukar ma'aikata guda 300 a watan Agustan shekarar 2025.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa Mimi Abu, darakta a ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, ita ce ta isar da amincewar gwamnatin na daukar ma'aikatan a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga Agusta, 2025.

Kara karanta wannan
Yadda shugaban ma'aikatar bogi ya rika tarurruka da manyan jami'an gwamnatin Tinubu
Wannan bada damar ya zama dole ne saboda takunkumin da gwamnatin tarayya ta sanya na dakatar da daukar ma'aikata a aikin gwamnati.
Ma'aikatan da aka amince a dauka
An dai bada damar ne a cikin wasika mai shafuka biyu da ke dauke da sanarwar bada damar, wadda aka aike da kofinta zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
A cikin wasikar, Mimi Abu ta ce an amince wa PFIPC ta dauki daraktoci guda 10 a kan matakin albashi na (GL) 17, da kuma mataimakan daraktoci guda 20 a kan matakin albashi na GL15.
An kuma ba da amincewar daukar jami'an gudanarwa guda 44, inda 20 suke kan GL08, 15 kan GL09, hudu kan GL12, sai kuma guda biyar kan GL14.
Adeyemi ya godewa Tinubu
Sa'o'i ashirin da hudu bayan fitar da wasikar, Adeniyi Adeyemi, babban daraktan PFIPC, ya wallafa sakon godiya a shafukan sada zumunta, inda ya gode wa Shugaba Bola Tinubu saboda ba da wannan damar.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"Mai girma shugaban kasa, muna samun ci gaba ne saboda ka amince da mu."

Kara karanta wannan
An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi
Adeyemi ya kuma nuna cewa hukumar ta samu amincewa na "kafa ofisoshin PFIPC a daukacin jihohi 36 na tarayya" da kuma "bude ofisoshi 127 a fadin duniya".
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"Wannan goyon baya mai hangen nesa yana kara karfafa kudurinmu na daukaka harkokin kasuwancin Najeriya da kuma janyo masu zuba jarin kasashen waje na kai tsaye ta kowace iyaka."

Source: Facebook
Ana takaddama kan hukumar PFIPC
Ce-ce-ku-cen ya fara ne a ranar 11 ga watan Yuni, lokacin da Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ya fitar da wata sanarwa da ke cewa PFIPC ba a san da zamanta a karkashin gwamnatin Tinubu ba.
Adeyemi ya kalubalanci wannan korafi, inda ya bukaci shugaban kasa da ya kafa kwamiti mai zaman kansa domin gudanar da bincike kan lamarin.
An dai warewa hukumar kudi Naira biliyan 1.3, wanda ya kunshi Naira miliyan 802.98 na albashi da alawus-alawus na ma'aikata, Naira miliyan 200 na gudanarwa, da kuma Naira miliyan 300 na manyan ayyuka a cikin kasafin kudin shekarar 2026.
Shugaban PFIPC ya yi magana
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ikirarin shugabancin hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi, ya yi magana kan nadin da aka yi masa.
Shugaban hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya dage cewa nadin da aka ba shi na gaskiya ne ba na bogi ba.
Adeniyi Adeyemi wanda ya shirya fuskantar shari'a, ya ce idan yana da laifi kotu ta hukunta shi, idan kuma ba shi da laifi kotu ta tabbatar da adalci.
Asali: Legit.ng
