Shugaban Majalisa Ya Nemi Afuwar Sanata, An Kashe Wutar Rikicin da Ta Dawo
- Godswill Akpabio ya ba Adams Oshiomhole hakuri game da sabanin da ya rika shiga tsakaninsu a majalisa
- Shugaban majalisar dattawan Najeriyan ya soki kalaman da sanatan ya yi kwanaki da ake bincike kan NNPCL
- Sanata Oshiomhole ya tuna wa Akpabio cewa sun yi yarjejeniyar zaman lafiya amma ya karya alkawarin da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya nemi afuwar abokin aikinsa daga jihar Edo, Adams Oshiomhole.
Godswill Akpabio ya ba shi hakuri saboda ya bayyana wasu kalaman Adams Oshiomhole da cewa ba su dace da na sanata ba.

Source: Getty Images
Rigimar Godswill Akpabio da Adams Oshiomhole
Leadership ta ce manyan ‘yan siyasar sun samu sabani ne lokacin da Akpabio yake zancen kalaman Oshiomhole kan binciken NNPC.
Lokacin da Sanata Oshiomhole ya dauki zafi game da zargin badakalar NNPC, sai aka ji ya ce a cafko Mele Kolo Kyari a raye ko a mace.
A zaman kwamiti da ke binciken asusun gwamnati, Sanatan na Edo ya fusata da tsohon shugaban na NNPCL ya ki bayyana gabansu.
Kwana guda da wannan barazana sai Sanata Opeyemi Bamidele ya nuna babu ruwan Majalisar dattawa da barazanar cafko Kyari da aka yi.
Lamarin ya kara munana a wata hira da aka yi da Oshimhole, sai ya fito yana zargin cewa Akpabio ya nema wa ‘yarsa aiki a kamfanin man.
Tsohon gwamnan Edo ya zargi shugaban majalisar da son kai da kokarin hana shi magana, wannan ya sa Akpabio ya maida martani.
Bidiyon Oshiomhole yana shafa kafar mace a jirgi
A ranar 16 ga watan Yuli 2026, sai aka ji Akpabio ya kawo zancen wani bidiyo da ake zargin Oshiomhole yana yi wa wata mata tausa.
Ana zargin Sanata Oshimhole ya rika shafa kafar wannan baiwar Allah a cikin jirgin sama. Da wannan zancen ne rikicinsu ya dawo danye.
Cikin wasa da dariya, tsohon shugaban kungiyar kwadagon na kasaya zargi Akpabio da saba wa yarjejeniyar zaman lafiyan da suka kulla.

Kara karanta wannan
An ji labarin abin da aka tattauna da Peter Obi ya zauna da Jakadan kasar Switzerland

Source: Getty Images
“Ina so in kawo kara a majalisar cewa ni da shugaban majalisa mun shiga yarjejeniya cewa ba za mu kara fada ba.
"Amma shugaban majalisa ya saba wannan yarjejeniya ta hanyar tado tsohon zance.
"Na fada wa shugaban majalisa cewa idan aka sa hannu, bai kamata ka saba alkawari ba. Kai ‘danuwa na ne, kai jagora na ne, kai shugaban majalisa ta ne."
- Adams Oshiomhole
Rahoto daga tashar Channels ya ce nan take a ranar Alhamis Akpabio ya ba Oshiomhole hakuri, ya ce bai yi hakan da nufin ya bata masa rai ba.
Akpabio ya maida wa Adams Oshiomhole amsa, yana cewa:
“Ka yi hakuri, mun yi yarjejeniya cewa an daina fada. Ba zan kara bayyana kalamanka da cewa ba su dace da sanata ba”
Sanatan Borno ya gargadi Ministan kudi
Sanata Muhammad Tahir Munguno ya koka game da matsalar aiwatar da kasafin kudi, an rahoto cewa ya fito yana sukar Ministan kudin Najeriya.
Mohammed Tahir Monguno ya kalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu dangane da jinkirin aiwatar da dokar kasafin kudin shekarar 2025.
'Dan majalisar ya tuna wa Taiwo Oyodele cewa za su iya tsige Tinubu idan har za a rika karyar ana samun kudi amma ba a san ina suke tafiya ba.
Asali: Legit.ng

