'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Bude wa Masu Koyon Karatun Kur'ani Wuta a Bauchi

'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Bude wa Masu Koyon Karatun Kur'ani Wuta a Bauchi

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kashe daliban makarantar allo tare da jikkata wasu a wani hari da suka kai kauyen Rafin Ciyawa a Bauchi
  • Maharan sun kuma yi garkuwa da mutum uku bayan sun kasa samun wasu mutane biyu da suke nema
  • Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ta ce ta tura jami'ai domin ceto wadanda aka sace da cafke 'yan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - 'Yan bindiga sun kashe daliban makarantar allo biyu, sun jikkata wasu shida tare da yin garkuwa da mutum uku a wani hari da suka kai kauyen Rafin Ciyawa da ke karamar hukumar Ningi a Jihar Bauchi.

Mazauna kauyen sun ce maharan sun afka musu ne da misalin karfe 12:30 na dare a ranar Laraba, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa al'umma cikin firgici.

Kara karanta wannan

Bam ya tarwatse da sojojin Najeriya a hanyar zuwa kai ɗauki, an rasa rayuka

Bauchi.
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda maharan suka kashe almajirai

Wani mazaunin kauyen, Zubairu Yahaya, ya ce da farko maharan sun bude wuta kan wasu yara almajirai da ke kwance a ƙofar gidan malaminsu na makarantar allo saboda tsananin zafi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya ce:

"Yara almajirai biyu sun mutu nan take, yayin da wasu shida suka samu munanan raunukan harbin bindiga."

Mahara sun sace yan gida daya

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce daga bisani maharan sun rika binciken gidaje domin neman wasu mutum biyu 'yan uwan juna, Saminu da Safiyanu, bisa zargin cewa sun karbi makudan kudade.

Da suka kasa samun su, sai suka yi garkuwa da wasu 'yan uwa su uku da aka bayyana sunayensu da Rukkaya, Samsiyya da Kabiru.

Masu garkuwa sun nemi kudin fansa

Mazauna yankin sun ce daga baya maharan sun tuntubi iyalan wadanda aka sace, inda suka rage kudin fansar da suke nema daga Naira miliyan 100 zuwa Naira miliyan 10.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi fito na fito da 'yan bindiga a Katsina, an rasa rayuka 8

Mukhtar Usman, wanda wasu daga cikin danginsa ke cikin wadanda aka sace, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da maharan.

Shugabannin al'umma sun bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Bauchi da su kafa sansanin jami'an tsaro na dindindin a yankin domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sanda cikin shirin aiki a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda sun fara bincike

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya ce rundunar ta tura jami'an Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane, tare da mafarauta da masu aikin sintiri na sa-kai domin ceto wadanda aka sace da kuma cafke wadanda suka aikata laifin.

Yan bindiga sun kai farmaki Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauye da ke karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare, inda suka kwashe kusan sa'a guda suna ta'asa.

Yayin harin, an samu da rahoton cewa 'yan bindigan sun kashe mazauna garin guda biyu tare da kwashe wasu da dama ciki har da jami'an 'yan sa-kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262