Kotu Ta Yanke Hukunci a Shari'ar da ke Kalubalantar Shugabancin David Mark a ADC
- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukunci a shari'ar da ke kalubalantar shugabancin David Mark a jam'iyyar ADC
- Alkalin kotun, mai shari'a Musa Liman ne ya yanke hukunci kan shari'ar a zaman da aka yi a ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026
- Alkalin kotun ya dai zartar da hukuncin ne a shari'ar wadda dan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar yana kalubalantar shugabancin David Mark
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci a shari'ar da ke kalubalantar shugabancin jam'iyyar ADC.
Babbar kotun tarayyar ta tabbatar da shugabancin Sanata David Mark a jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa alkalin kotun, mai shari'a Musa Liman, ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026. kotun, mai shari'a Musa Liman, ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan
NNPP ta gamu da matsala, INEC ta hana ta tura sunayen 'yan takararta na zaben 2027
Wane hukunci kotu ta yanke?
A cikin hukuncinsa, mai shari'a Musa Liman ya kuma yi watsi da karar da Leke Abejide ya shigar yana kalubalantar David Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam'iyyar ADC na kasa saboda rashin hujjoji.
Mai Shari'a Liman ya amince da hujjojin ADC, Cif Ralph Nwosu, David Mark, da Aregbesola suka shigar, wadanda suka kalubalanci karar ta Abejide.
Alkalin ya bayyana cewa kotun ba ta da ikon tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ADC, kasancewar karar ba wadda kotu za ta iya yanke hukunci a kanta ba ce.
An gano kuskure a karar da aka shigar
Ya kuma bayyana cewa Leke Abejide ba ya da hakki na shari'a na shigar da karar, duba da cewa ya kasa nuna wa kotu cewa an keta hakkinsa ta kowace hanya sakamakon shugabancin da David Mark ke jagoranta, rahoton Daily Post ya nuna hakan.
Haka zalika, ya bayyana cewa Leke Abejide, wanda mamba ne a Majalisar Wakilai, ya kasa amfani da hanyoyin cikin gida na jam'iyyar domin sasanta rashin jituwar.
Mai shari'a Musa Liman ya kuma warware batutuwa guda uku da ke cikin ainihin karar domin amfanin wadanda ake kara.
Ya bayyana cewa mika shugabancin jam'iyyar da Ralph Nwosu ya yi ga David Mark bai sabawa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba.
An tabbatar da shugabancin David Mark
Sakamakon haka, mai shari'a Musa Liman ya ayyana cewa zaman David Mark da Aregbesola a matsayin shugabannin ADC yana da inganci kuma ya dace da kundin tsarin mulki, dokar zabe ta 2026, da kuma dokar jam'iyyar.
Daga karshe, alkalin ya yanke a biya tarar Naira miliyan 2 ga daukacin wadanda ake kara, wadda Leke Abejide zai biya.

Source: Twitter
Alkalin kotun ya kuma yanke tarar Naira miliyan 10 ga lauyan Abejide daidai da dokar zabe ta 2026.
Leke Abejide ya shigar da karar ne domin dakatar da shugabancin ADC da Mark ke jagoranta.
Jigon ADC ya taka wa Nyesom Wike birki
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar ADC, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya yi watsi da kalaman da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi kan Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC
Eze ya nuna damuwa kan cewa Wike ya yi ikirarin yana da tsarin siyasa da zai tabbatar da cewa Atiku ya sake shan kaye a zaben shugaban kasa na 2027.
Jigon na jam'iyyar ADC ya kalubalanci Ministan Abuja da ya bayyana irin "tsarin siyasa" da yake yawan ambata a jawabansa.
Asali: Legit.ng
