Baya Ta Haihu, Masu Neman Takara a APC Sun Nemi a Mayar Masu Kudinsu
- Masu neman takarar APC a Majalisar Dokokin jihar Kwara sun nemi a mayar masu da kuɗin da suka kashe bayan zaɓen fitar da gwani
- Sun ce an hana wasu shiga zaɓen fitar da gwanin duk da cewa shugabancin APC na ƙasa ya tantance su kuma an ba suu damar neman takara
- Ƙungiyar masu neman takarar ta buƙaci a biya kowannensu diyya ko a samar masu da wata mafitata siyasa yayin da ke kokarin yin sulhu a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kwara - Wasu masu neman tikitin takarar jam'iyyar APC domin kujerun Majalisar Dokokin Jihar Kwara a zaben 2027 sun bukaci jam'iyyar ta mayar masu da kuɗin da suka kashe wajen sayen fom, kamfen da sauransu.
Ƙungiyar masu neman takarar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar bayan ta yi nazari kan yadda aka gudanar da zaɓen fitar da gwani na 'yan takarar majalisar dokoki da kuma matakan sulhun da ake yi a cikin jam'iyyar APC a jihar.

Source: Twitter
Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban ƙungiyar, Hon. Cif Olu Adewara, tare da mataimakansa daga yankunan Kwara ta Kudu, Tsakiya da Arewa, da sauran manyan jami'anta ne suka sanya hannu kan sanarwar.
Masu neman takarar APC sun fusata
Channels TV ta kawo labarin cewa kungiyar ta yi zargin cewa shugabancin APC na jihar ya hana wasu daga cikin masu neman takarar shiga zaɓen fitar da gwani bayan ya bayyana cewa ba su cika sharuddan takara ba.
Sai dai ta ce mutanen da abin ya shafa sun sayi fam, sun halarci tantancewa, kuma shugabancin APC na ƙasa ya amince da su kafin daga bisani aka hana su shiga zaɓen fitar da gwani.
A cewar ƙungiyar, wannan mataki zalunci ne na siyasa da ya hana mambobin jam'iyyar masu biyayya damar gwada farin jininsu a gaban wakilan zaɓe duk da shekarun da suka shafe suna hidima da kuma kuɗin da suka zuba a jam'iyyar.
Matsayar masu neman takara a APC
Ta ce duk da cewa har yanzu tana goyon bayan haɗin kan APC, bai kamata a saka wa biyayya da nuna wariya ba ko kuma a mayar da sadaukarwa da watsi.
Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin APC su sake duba yadda aka hana waɗannan masu neman takara shiga zaɓen fitar da gwani tare da mutunta amincewar da shugabancin jam'iyyar na ƙasa ya ba su tun farko.

Source: Original
Haka kuma ta roƙi jam'iyyar ta yi la'akari da bai wa wasu daga cikinsu damar samun tikitin wasu muƙaman zaɓe idan akwai hali.
Baya ga haka, ta buƙaci APC ta ba waɗanda ba su samu damar tsayawa takara ba muƙaman siyasa, shugabancin kamfen, kujeru a hukumomi da kwamitoci ko wasu nauyin gwamnati.
Sanatan APC ya sauya sheka
A baya, mun kawo maku cewa Sanatan jam'iyyar adawa, Olubiyi Fadeyi ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC watanni 12 da sauya shekarsa saboda an gaza cika alkawari.
Sanatan mai wakiltar mazabar Osun ta Tsakiya ya bayyana cewa akwai rashin dimokuraɗiyya da kuma samun sabani da shugabancin jam'iyyar a jiharsa, yayin da sauran takwarorinsa su ka haye
Duk da sauya jam'iyya, Fadeyi ya jaddada cewa har yanzu yana goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manufofin gwamnatinsa tare da duk mai yiwu wa wajen ci gaba da ganin ci gabansa.
Asali: Legit.ng


