Yadda aka Kafa Ma'aikatar Bogi a Najeriya ba tare da Tinubu Ya Gano ba

Yadda aka Kafa Ma'aikatar Bogi a Najeriya ba tare da Tinubu Ya Gano ba

  • Rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban kasa ta wanke Femi Gbajabiamila daga zargin cin hanci da aka yi masa bayan ce-ce-ku-ce
  • Mai magana da yawun Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya ce wanda ya yi zargin, Prince Adeniyi Adeyemi, ya yaudari CBN sauran hukumomi
  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa hukumar da Adeyemi ke ikirarin jagoranta ta bogi ce, ya kafa ta ba tare da sanin hukumomin kasar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Fadar shugaban kasa ta wanke shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, daga zargin neman cin hanci da Prince Adeniyi Adeyem ya yi.

Adeyem na ikirarin shi ne shugaban hukumar bunƙasa tallafin kasashen waje ta fadar shugaban kasa, inda ya bude ofis kuma ya gana da hukumomin Najeriya da dama.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar N400m: Atiku ya bukaci Tinubu ya kori shugaban ma'aikatansa

Adeniyi Adeyemi da ya zargi jami'in Bola Tinubu
Adeniyi Adeyemi da ake zargi ya kafa ma'aikatar bogi a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a Facebook, mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya nuna cewa gwamnati ba ta san da zaman Adeniyi ba a hukumance.

Zargin Adeyemi kan Gbaja

Adeyemi ya zargi Gbajabiamila da neman tallafin fara aiki na hukumar har Naira biliyan 27.39, zargin da tsohon shugaban majalisar wakilai ya musanta.

Ya kuma yi zargin cewa Gbajabiamila ya karɓi Naira miliyan 400 ta hannun wasu domin tabbatar masa da naɗin shugaban hukumar, inda ya ce akwai kudin da bai riga ya biya ba har yanzu.

Ya ce rashin jituwarsu ya samo asali ne daga wannan kuɗin da ya rage, tare da roƙon shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken lamarin.

An kafa ma'aikatar bogi a Najeriya

Daily Trust ta rahoto cewa wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Laraba, ta zargi Adeyemi da yaɗa ƙarya kan zarge-zargen da ya yi.

Kara karanta wannan

Masoyin Tinubu ya hango matsala, ya magantu kan tsawaita wa'adin shugaban Kwastam

Ya ce Adeyemi yana gabatar da kansa a matsayin shugaban wata hukuma ta bogi da shugaban kasa bai san da zaman ta ba.

Onanuga ya ce ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ne ya fara tona asirin wannan haramtacciyar hukuma ta Adeyemi.

Ya ce Gbajabiamila ya rubuta wa DSS da 'yan sanda wasiƙa yana neman su binciki wasu masu damfara da ke ƙirƙirar takardun naɗin mukami na bogi da sunan ofishinsa.

Femi Gbajabiamila da aka zarga
Hdimin Bola Tinubu, Femi Gbajabiamila da ake zargi da neman na goro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Binciken da aka gudanar

Onanuga ya ce binciken 'yan sanda ya tabbatar da cewa hukumar da Adeyemi ke ikirarin jagoranta ta bogi ce, kuma ya ƙirƙiri takardar naɗinsa ta bogi tare da wasu takardu da aka samu a gidansa da ofishinsa.

A cewar Onanuga, 'yan sanda sun gano cewa Adeyemi ya gudanar da asusun banki 34, ciki har da guda tara da aka buɗe da sunayen hukumomin bogi.

Ya ce binciken ya kuma gano cewa Adeyemi ya yi amfani da takardun bogi wajen buɗe asusun CBN bayan ya yaudari Ofishin Akanta Janar na Tarayya, amma babu wani kuɗin gwamnati da aka taɓa turawa cikin wannan asusun.

Kara karanta wannan

"Ba ka isa ba," Jigon ADC ya takawa Wike birki kan wanda zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Tinubu zai ciwo abon bashi

A wani labarin, mun kawo muku cewa bankin duniya ya amince zai ba shugaban kasa Bola Tinubu bashin kudi har dala biliyan 1.25.

Rahotanni sun nuna cewa bankin ya ce za a yi amfani da kudin ne domin yin ayyukan da suka shafi raya kasa kamar samar da lantarki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da korafi kan yawan bashin Najeriya duk da ya karu sosai bayan zuwan Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng