Siyasar Najeriya
Idan za’a tuna an samu cacar baki da musayar yawu tsakanin Sanata Kwankwaso da shugaban kungiyar Izala reshen jahar Kano, Sheikh Abdallah Saleh Pakistan akan dan takarar da yafi cancanta Kanawa su zaba a mukamin gwamna.
Mun ji cewa Atiku ya bayyana ainihin abin da ya sa ya shiga siyasa a Najeriya. Atiku yace abin da yake so shi ne ya ga wanda ba ‘Dan kowa ba ya zama kowa. Atiku yace wannan shi ne babban burin da yake ke da shi a siyasar Najeriya.
Mun samu cewa, a yayin da gwamnatin jihar Akwa Ibom karkashin jagorancin gwamna Udom Emmanuel ta daura damarar samar da kamfanin jiragen sama na karan kanta, a yau Laraba tsala-tsalan jiragen sama biyu sun dira a birnin Uyo.
Mun samu cewa, a jiya Talata, 19 ga watan Fabrairun 2019, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya yiwa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar yakin neman zabe a jihar Legas.
Gamayyar kungiyoyin siyasar Najeriya (CUPP) ta yaba wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) bisa fitar da sanarwar nesanta tsohon shugabanta, Lawal Daura, da aiyukan hukumar. Kzalika, CUPP ta yi kira ga hukumar DSS da ta tabbatar ta
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya daura damara ta shiga tsakani domin warware rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara.
Al-Mustapha ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace akwai bukatar yan Najeriya su dauki gyaran kasar tamkar gyaran Mota, saboda idan zaka gyara motarka baka bukatar wani kabila, kwararre kawai
Rundunar Sojan kasan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari daya bayar na bindige duk wani ko wasu da aka kama suna kokarin sace akwatin zabe a babban zaben kasar da zai gudana a mako mai zuwa.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC reshen jihar Neja, ta karbe tikitin takarar kujerar wakilin shiyyar Neja ta Gabas na majalisar dattawa daga hannu Sanata David Umaru ta kuma danka shi a hannun Muhammad Sani Musa.
Siyasar Najeriya
Samu kari