Siyasar Kano: Sheikh Daurawa ya bayyana dalilin daya jagoranci Malamai 100 zuwa gidan Kwankwaso

Siyasar Kano: Sheikh Daurawa ya bayyana dalilin daya jagoranci Malamai 100 zuwa gidan Kwankwaso

Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jahar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana dalilin da yasa ya jagoranci Malamai gudsa dari zuwa gidan tsohon gwamman jahar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso a gidansa.

Daurawa ya bayyana ma jaridar Daily Trust dalilin ne a wata hirar wayar tarho da yayi da ita a ranar Laraba, 20 ga watan Feburairu, inda yace sun kai ma Kwankwaso ziyarar ne da nufin sulhunta tsakaninsa da wasu Malaman addinin Musulunci a jahar.

KU KARANTA: An bude jami’ar Sojoji da sama da dalibai 1000 a jahar Borno

Siyasar Kano: Sheikh Daurawa ya bayyana dalilin daya jagoranci Malamai 100 zuwa gidan Kwankwaso

Daurawa
Source: UGC

Idan za’a tuna an samu cacar baki da musayar yawu tsakanin Sanata Kwankwaso da shugaban kungiyar Izala reshen jahar Kano, Sheikh Abdallah Saleh Pakistan akan dan takarar da yafi cancanta Kanawa su zaba a mukamin gwamna.

Duk da cewa akwai rade radin Gwamna Ganduje zai tsige Daurawa daga mukaminsa, amma a jawabinsa, Daurawa yace sun kai ziyarar ne domin kwantar da hankulan da suka tashi sakamakon wancan takaddama tsakanin Malamai da Kwankwaso.

“Mun samu labarin Malamai sun yanke hukuncin caccakar Kwankwaso a akan mumbarin huduba, haka zalika suma yan Kwankwasiyya sun dauki alwashin mayar da martani akan Maluman, don haka muka ga dacewar shiga tsakani a matsayinmu na Malamai.

“Mun samu nasara saboda yan Kwankwasiyya basu mayar da martani ba duk kuwa da cewa Malaman sun yi hudubar tasu.” Kamar yadda Daura ya bayyana, sai dai game da sallamarsa daga aiki kuwa, Daurawa ya bayyana rashin wata masniya game da hakan.

“Kafin na tafi Umarah, na mika makullin ofishina ga kwamandan Hisbah na biyu, kuma babu wanda ya kirani ya bayyana min wani abu game da kulle ofishina ko sauya ma sakatarena wajen aiki, kuma babu wata wasikar sallama da aka bani, muna ji muna gani muna kuma sauraron gwamnati.” Inji shi

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel