Sama ko kasa: An nemi kuri'u 6,053 an rasa a jihar Ogun - ADC

Sama ko kasa: An nemi kuri'u 6,053 an rasa a jihar Ogun - ADC

Jam'iyyar African Democratic Congress ADC reshen jihar Ogun ta bukaci kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Abdulganiyu Raji ya fito da sauran takardun dangwale kuri'a 6,053 da su kayi karanci a cikin kuri'un zaben 'yan majalisar wakilai na karamar hukumar Afon a jihar.

A cikin takardar korafi da suka aike wa Raji, jam'iyyar tayi ikirarin cewa cikin takardun dangwale kuri'a 62,853 na zaben yankin, 6,053 sun bace.

Shugaban jam'iyyar ADC na karamar hukumar, Kayode Elegbede da dan takarar majalisar Wakilai na maganar, Jimoh Aremu Olaifa suna daga cikin wadanda suka sanya hannu a kan karar.

Kuri'u 6,053 sun bace a jihar Ogun
Kuri'u 6,053 sun bace a jihar Ogun
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja

Sun bukaci Kwamishinan zaben ya fito da kuri'un da su kayi saura a cikin gaggawa domin tabbatar da zabe sahihiya.

Da aka tuntube shi, jami'in wayar da kan masu zabe na jihar, Mrs Adenike Tadese ta tabbatar da karancin kuri'un da aka samu amma ta ce ba abin damuwa bane.

"Ba a bude kwalin ba, sai lokacin da aka isa karamar hukumar sannan aka gano takardun dangwale kuri'un basu kai ba.

"Jami'in zabe na karamar hukumar ya kira taron masu ruwa da tsaki domin yi musu bayanin abinda ya faru.

"Saboda haka babu wata kumbiya-kumbiya da aka shirya. Mun sanar da hedkwata domin a turo mana abinda ya yi saura kuma za a turo, babu wata matsala a yanzu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel