Da dumin sa: ‘Yan dabar siyasa sun saka wa gidan Abdulmuminu Kofa wuta a Kano, bidiyo

Da dumin sa: ‘Yan dabar siyasa sun saka wa gidan Abdulmuminu Kofa wuta a Kano, bidiyo

Labarin da jaridar Legit.ng ke samu daga jihar Kano sun tabbatar ma ta da cewar wasu ‘yan dabar siyasa sun saka wuta a gidan dan majalisar tarayya mai wailtar mazabar Kiru da Bebeji, Abdulmuminu Jibrin Kofa, a garin Kofa da ke karamar hukumar Bebeji.

Majiyar mu ta shaida ma na cewar an saka wa gidan Kofa wuta ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP karkashin jagorancin madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ke gudanar da taron kamfen a karamar hukumar Bebeji.

Labarin saka wuta a gidan dan majalisar na zuwa ne a daidai lokacin d wasu kafafen yada labarai su ka wallafa cewar wasu 'yan bangar siyasa sun kai wa tawagar yakin neman zaben da sanata Kwankwaso ke jagoranta hari. Rahotannin sun ce mutane da dama sun mutu sakamakon harin.

DUBA WANNAN: An kai wa tawagar dan takarar sanata a APC hari

Sai dai a faifan bidiyon da ke cikin wannan labarin, an ji muryar wasu na bayyana cewar 'yan Kwankwasiyya ne su ka saka wuta a gidan Kofa da gidajen wasu ragowar 'yan jam'iyyar APC.

Kazalika, an ji suna fadin cewar magoya bayan Kwankwasiyyar sun kona motoci tare da kashe wasu mutane. Sai dai, majiyar mu ba ta sanar da mu faruwar hakan ba.

Babu wata sanarwa ko jawabi daga rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ko kuma daga bangaren Kofa ko Kwankwasiyya ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel