2027: Kwankwaso Ya Tsallake NDC, Ya Sayi Fam din Takara a Jam'iyyar PRP? Gaskiya Ta Fito
- Jam’iyyar PRP ta musanta rade-radin cewa madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya sheka zuwa cikinta
- Sakataren PRP ya musanta zargin cewa Kwankwaso ya sayi fom 69 na takara domin karbe ragamar jam'iyyar kafin zaben 2027
- Jam’iyyar ta ce an kammala dukkan zabukan fitar da gwani kuma babu sauran fom da ake sayarwa a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - PRP ta karyata zargin cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sayi fom din takara guda 69 domin karbe ragamar jam’iyyar gabanin babban zaben 2027.
Sakataren jam’iyyar, Musa Maigari, ne ya yi wannan bayani yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni, 2026.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa Kwankwaso ba mamba ba ne a PRP, kuma an riga an kammala dukkan matakan tantance ‘yan takara a jam’iyyar, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
Jam'iyyar PRP ta maida martani
Martanin Maigari ya biyo bayan zargin da Abdulkadir Guza ya yi cewa Kwankwaso ya sayi fom din takara guda 69 na PRP da nufin karbe tsarin jam’iyyar kafin babban zabe mai zuwa.
Sai dai sakataren jam’iyyar PRP ya bayyana zargin a matsayin mara tushe kuma maras inganci, yana mai cewa an riga an cike dukkan mukaman takara ta hanyar zabukan fitar da gwani.
Ya ce:
“A halin yanzu, mun gama tsaida yan takara a dukkan mukamai a PRP. An kammala zabukan fidda gwani, kuma jam’iyyun siyasa sun gama gudanar da nasu zabukan.”
Kwankwaso ya shiga jam'iyyar PRP?
Maigari ya kuma yi tambaya kan sahihancin zargin, yana mai cewa mutumin da ya fito da batun ba mamban jam’iyyar PRP ba ne, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
“Mutumin da ya yi wannan zargi ba ma mamban jam’iyyarmu ba ne. Abin dariya ne a wannan lokaci da aka riga aka kammala zabukan fitar da gwani, a ce ana magana kan fom din takara," in ji shi.
Sakataren PRP ya kara da cewa babu wani bayani a hedikwatar jam’iyyar da ke nuna cewa Kwankwaso ko wakilansa sun taba sayen wani fom na takara daga jam’iyyar.
A cewarsa, lokacin da aka kawo zargin ma ya kara jefa shakku, domin ya zo ne bayan jam’iyyar ta kammala zabukan fitar da gwani domin shirye-shiryen zabe mao zuwa.

Source: Facebook
PRP ta aika sako ga 'yan Najeriya
Maigari ya bukaci jama’a su yi watsi da abin da ya kira jita-jita mara tushe, tare da shawartar magoya bayan PRP da sauran al’umma su daina daukar irin wadannan labaran.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bangaren Kwankwaso bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan zargin da Guza ya yi.
Kwankwaso ya yi maraba da tsarin NDC
A wani rahoton, kun ji cewa Kwankwaso ya goyi bayan sabuwar dokar jam’iyyar NDC da za ta hana ’yan siyasa sauya sheƙa bayan sun ci zaɓe a.karkashin inuwarta.
NDC dai ta bullo da wata sabuwar doka da za ta tilasta wa ’yan takararta sanya hannu kan takardar rantsuwa da ke tabbatar da cewa za su mika kujerunsu idan suka sauya sheka bayan sun ci zabe.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya nuna goyon bayansa ga wannan tsari, yana mai cewa ya dace da abin da suka daɗe suna kira a kai, wato biyayya ga jam’iyya da mutunta ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Asali: Legit.ng

