Da dumi dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da aka kai ma Kwankwaso hari a jahar Kano

Da dumi dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da aka kai ma Kwankwaso hari a jahar Kano

Wani rahoton da muka samu da dumi dumi ta ruwaito wasu matasa yan daba sun kai ma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a daidai kauyen Kofa cikin karamar hukumar Bebeji ta jahar Kano, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kwashi gawarwakin mutane da dama daga bangaren magoya bayan Kwankwaso wanda aka fi saninsu da suna yan Kwankwasiyya da kuma bangaren yan daban da suka kai masa harin, haka zalika jama’a da dama sun jikkata.

KU KARANTA: Siyasar Kano: Sheikh Daurawa ya bayyana dalilin daya jagoranci Malamai 100 zuwa gidan Kwankwaso

Da dumi dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da aka kai ma Kwankwaso hari a jahar Kano
Rikicin
Source: Facebook

Da fari dai Sanata Kwankwaso ya shirya karkare yakin neman zaben da yake taya dan takarar gwamnan jahar Kano na jam’iyyar PDP, kuma dan darikar Kwankwasiyya, Abba K Yusuf a garuruwan Kiru da Bebeji a ranar Alhamis, 21 ga watan Feburairu.

Sai dai wasu majiyoyi sun danganta yan daban da suka kai ma Kwankwaso harin ga yaran dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji, Abdulmuminu Jibrin, wadanda suka tare ma Kwankwaso hanya.

Da dumi dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da aka kai ma Kwankwaso hari a jahar Kano
Rikicin
Source: Facebook

Majiyarmu ta tabbatar da an kona akalla motoci guda goma kurmus a yayin rikicin siyasan, haka zalika kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kaakakin yace sun samu rahoton rikicin daya barke tsakanin bangarorin siyasa guda biyu masu hamayya da juna, kuma tuni suka aika da jami’ansu domin su kwantar da tarzomar tare da kwantar da hankulan jama’a.

Sai dai kaakaki Abdullahi Haruna yace basu da tabbacin adadin mutanen da aka kashe da wadanda suka samu rauni, har zuwa lokacin tattara wannan rahoto. Idan za’a tuna a yan kwanakin nan ne aka jiyo mai martaba Sarkin Kano yana kira ga yan siyasa da su ji tsoron Allah kada su jefa jahar Kano cikin rikici.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel