Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana hanya daya da za’a bi don gyara Najeriya

Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana hanya daya da za’a bi don gyara Najeriya

Tsohon babban dogarin tsohon shugaban kasan Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana hanya daya daya kamata yan Najeriya su bi wajen gyaran kasar tare da karkatar da ita zuwa ga tudun mun tsira.

Al-Mustapha ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace akwai bukatar yan Najeriya su dauki gyaran kasar tamkar gyaran Mota, saboda idan zaka gyara motarka baka bukatar wani kabila, kwararre kawai kake nema.

KU KARANTA: Rundunar Sojan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin Buhari akan barayin akwatin zabe

Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana hanya daya da za’a bi don gyara Najeriya
Manjo Hamza Al-Mustapha
Asali: Facebook

Haka zalika Al-Mustapha ya koka kan yadda amma idan lamari ya shafi mulki ne a Najeriya, sai kaga kowa na neman dan uwansa ya samu koda kuwa bai cancanta ba, sai don kawai addininsu daya, ko kabilarsu daya.

“Idan lamari ne daya shafi yi ma Najeriya hidima, sai mu fara neman dan kabilarmu, koda bai cancanta ba, amma idan motarmu ta lalace bama neman Musulmi ko Kirista, Bahaushe ko Bayarabe, kwararren bakanike kawai muke nema don ya gyara mana.

“Har sai lokacin da muka fara neman gyaran Najeriya tamkar yadda muke gyara motocinmu, ba zamu taba rabuwa da matsalolinmu a Najeriya ba, yanzu muka fara ganinsu.” Inji shi.

Idan za’a tuna a shekarar 2014 ne kotun koli ta wanke Al-Mustapha daga tuhume tuhumen da ake yi masa na zargin hannu cikin kisan uwargidar marigayi MKO Abiola, Kudirat Abiola, bayan kwashe sama da shekaru goma sha biyar yana daure.

Rahotanni sun bayyana Al-Mustapha ya taka muhimmiyar rawa a zamanin mulkin marigayi janar Sani Abacha daga shekarar 1993 zuwa 1998, inda har wasu suka yi masa kiraye kirayen ya dare mulkin Najeriya bayan mutuwar Sani Abacha, amma yaki, ya mika mulki ga Janar Abdulsalam Abubakar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel