Kasar Amurka ta rufe ofisoshinta dake Legas da babban birnin tarayya Abuja

Kasar Amurka ta rufe ofisoshinta dake Legas da babban birnin tarayya Abuja

Gwamnatin kasar Amurka ta garkame ofisoshin jakadancinta dake jahar Legas da wanda ke babban birnin tarayya Abuja, wannan ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin Najeriya ta yi na cewa babu aiki a ranar Juma’a, 22 ga watan Feburairu.

Legit.ng ta ruwaito Amurka ta bayyana haka ne ciki wata sanarwa data fitar a ranar Juma’a, inda tace ta rufe ofisoshinne domin baiwa yan Najeriya dake aiki a ofisoshin damar shirye shirye tare da kada kuri’unsu a zaben kasar da za’ayi a ranar Asabar.

KU KARANTA: Ina mazan suke: Yadda wasu Mata suka yi arangama da masu garkuwa da mutane suka samu nasara

Kasar Amurka ta rufe ofisoshinta dake Legas da babban birnin tarayya Abuja
Kasar Amurka ta rufe ofisoshinta dake Legas da babban birnin tarayya Abuja
Asali: UGC

Don haka kasar Amurka take shawartar duk abokan huldarta da suke da nufin zuwa wani daga cikin ofishinta a ranar Juma’a dasu dakata har sai bayan zabe, haka nan ofishin jakadancin ta yi alkawarin kiran duk wadanda ta tsara ma gayyata a ranar Juma’a ta wayar salula don canza musu rana.

“Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Juma’a, 22 ga watan Feburairu a matsayin ranar da babu aiki don baiwa yan Najeriya damar shiryawa da kuma shiga zaben shugaban kasa da na yan majalisu da za’ayi a ranar Asabar.

“Duba da wannan sanarwa, da kuma burinmu na baiwa ma’aikatanmu yan Najeriya kwarin gwiwar su aiwatar da yancinsu na zabe yasa muka kulle ofisoshin jakadancinmu dake Abuja da Legas.” Inji sanarwar.

Idan za’a tuna tun a ranar Laraba ne gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar hutu don baiwa yan kasa dama shirya ma zaben ranar Asabar, sai dai sanarwa ta cire bankuna da ma’aikatanta daga cikin wadanda zasu yi hutun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel