CUPP ta bukaci DSS ta kama Lawal Daura saboda yin sojan gona

CUPP ta bukaci DSS ta kama Lawal Daura saboda yin sojan gona

Gamayyar kungiyoyin jam'iyyun adawar siyasar Najeriya (CUPP) ta yaba wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) bisa fitar da sanarwar nesanta tsohon shugabanta, Lawal Daura, da aiyukan hukumar.

Kazalika, CUPP ta yi kira ga hukumar DSS da ta tabbatar ta kama Lawal Daura tare da gurfanar da shi a kan aikata laifin sojan gona da kuma zamba.

Kakakin CUPP, Imo Ugochinyer, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba ga manema labarai a yau, Talata.

Ugochinyere ya bukaci DSS ta gaggauta cire dukkan darektocin hukumar da ke biyayya ga Lawal Daura.

Jam’iyyun adawa sun yaba wa babban darektan hukumar tsaro ta DSS bisa fitar da sanarwar shaida wa duniya cewar tsohon shugaban hukumar na karbar kudi daga hannun wasu mutane ta hanyar yin sojan gona a matsayin babban darektan hukumar DSS.

CUPP ta bukaci DSS ta kama Lawal Daura saboda yin sojan gona

Lawal Daura
Source: UGC

“Mu na sane da kitimurmurar da wasu a fadar shugaban kasa ke shirya wa da Lawal Daura domin ganin an tsige shugaban gukumar DSS saboda ya ki amince wa a yi amfani da hukumar sa domin kama ‘yan jam’iyyar adawa,” a cewar Ugochinyer.

Ugochinyere ya bayyana cewar har yanzu Daura na sarrafa wasu manyan jami’an hukumar DSS, kuma hakan ne ya bashi damar kafa tsagin hukumar DSS da ya ke ikirarin ya na shugabanta.

DUBA WANNAN: Zabe: ‘Yan sanda sun kama wani mutum da kuri’un bogi a Sokoto

Ya kara da cewa, “a saboda haka mu na kira da a gaggauta cire dukkan manyan darektocin hukumar DSS da ke biyayya ga umarnin da Daura ke ba su daga gidan sa.

“Shugaban hukumar DSS ya nuna cewar shi mutum ne mai yin aiki da doka da tsarin aiki. A saboda haka, jam’iyyun adawa na yin kira ga hukumar DSS da ta kama Lawal Daura domin gurfanar da shi bisa aikata laifukan zamba da sojan gona,” a kalaman Ugochinyere.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel