Andy Burnham: 'Dan Siyasar da Ake Hasashen Zai Zama Firayim Ministan Birtaniya
Birtaniya — Andy Burnham, wanda aka fi sani da “Sarkin Arewa,” ya zama ɗan takarar da ake ganin zai gaji kujerar Firayim Ministan Birtaniya bayan murabus ɗin Sir Keir Starmer daga Downing Street.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bayan manyan jiga-jigan Jam’iyyar Labour ciki har da Wes Streeting sun nuna goyon baya gare shi, hanyar Burnham zuwa shugabanci na ƙara bayyana cikin sauƙi yayin da jam’iyya ke shirin fara sabon zaɓen shugaba.

Source: Getty Images
Amma wanene Andy Burnham, kuma ta yaya ya kai ga zama mutum mafi kusa da kujerar Firayim Minista? Jaridar The Independent ta amsa wadannan tambayoyi a rahoton da ta fitar.
Rayuwa da fara siyasar Burnham
Andy Burnham ya kasance ɗa ga injiniyan BT, da kuma mahaifiya da ke aiki a ofis, kuma ya taso cikin rayuwar talakawa a Birtaniya.
Ya shiga Jam’iyyar Labour tun yana da shekaru 15, inda daga bisani ya yi karatu a jami'ar Cambridge, kuma ya fara hawan matakan siyasa cikin sauri.
Bayan ya fara aiki a matsayin mai taimaka wa Chris Smith lokacin New Labour, Burnham ya fara samun matsayi a siyasa.
Bayan zaɓensa a matsayin ɗan majalisa a 2001 daga mazabar Leigh, ya rike muƙamai daban-daban har ya zama ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan Labour.
Mukaman da Burnham ya rike
Burnham ya rike muƙamai a gwamnati a lokacin Tony Blair da Gordon Brown, inda ya yi aiki a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da kuma Ma’aikatar Lafiya.
Daga bisani, ya zama babban minista a ma’aikatar kuɗi, kuma daya daga cikin masu fada aji a majalisar ministoci, cewar rahoton BBC.
Sai dai mafi shaharar rawar da ya taka ita ce lokacin da ya zama Ministan Al’adu, inda ya jagoranci gwagwarmayar neman adalci ga waɗanda suka sha wahala a rikicin Hillsborough — wanda ya ƙara masa farin jini a ƙasa.
Zama magajin garin Greater Manchester
A shekarar 2017, Burnham ya bar majalisar dokoki, inda ya ce siyasar Birtaniya ta koma mai cike da matsala da rashin daidaito tsakanin London da sauran yankuna.
Bayan haka, ya zama na farko da aka zaɓa a matsayin magajin garin Greater Manchester, inda ya samu sama da kashi 60 na kuri’u.
A matsayin magajin gari, ya ƙara karfi wajen inganta sufuri, gidaje da walwalar jama’a a yankin arewacin Ingila, kamar yadda rahoton UK Parliament ya nuna.
A kwanan nan, Burnham ya nuna sha’awar komawa majalisar tarayya domin taka rawa kai tsaye a shugabancin ƙasa.
Ya kuma soki yadda Jam’iyyar Labour ke tafiya a karkashin Firayim Minista Keir Starmer, yana mai cewa akwai babban gibi tsakanin siyasar Westminster da talakawa.

Source: Getty Images
Hanyar Burnham zuwa Downing Street
A lokacin da Starmer ya sanar da murabus dinsa, masana sun ce 'yar manuniya ce ta nuna cewa Burnham zai tsaya takarar shugabancin Labour.
Masu sharhi kan siyasa na ganin cewa yana da damar zama Firayim Minista cikin makonni masu zuwa, idan ya samu nasara a cikin jam’iyya.
Sai dai har yanzu ana tambaya ko goyon bayan da yake da shi a arewacin Ingila zai iya isa ya ba shi rinjaye a fadin ƙasar.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano
Firayim Ministan Birtaniya ya yi murabus
A wani labari, mun ruwaito cewa, Firayim Ministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, ya sanar da murabus daga mukaminsa bayan ya shafe ƙasa da shekaru biyu a kan mulki.
Starmer ya bayyana cewa za a fara zaben sabon shugaban Jam’iyyar Labour a watan Yuli, yayin zai ci gaba da rike mukamin Firayim Minista.
Murabus ɗin ya biyo bayan watanni na rikice-rikicen siyasa, sauyin manufofi, raguwar farin jini a wajen jama’a, da kalaman Donald Trump.
Asali: Legit.ng

