Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala

Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala

Hadakan shugabanin matasa na jam'iyyun siyasa a Najeriya sunyi shirin sanar da goyon bayan su ga dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar a yau Alhamis sai dai an samu matsala a kan adadin jam'iyyun da a farko suka ce za su marawa Atiku baya kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Jam'iyyun siyasa biyar ne suka shirya sanar da goyon bayan su ga Atiku a yammacin yau Alhamis sai dai daya daga cikin jam'iyyun ta janye.

Shugaban matasa na Kowa Party ya aike sakon e-mail ga majiyar Legit.ng inda ya ce Kungiyar shugabanin matasa na jam'iyyun siyasa (CONYLOP) za ta kira taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja.

A cewarsa sakon da Olawole ya aike, za a kira taron manema labaran ne domin bayyana goyon bayansu da dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

DUBA WANNAN: Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala
Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala
Asali: Twitter

Sai dai an samu rudanni saboda wasu daga cikin shugabanin matasa na jam'iyyun siyasan suna tantama a kan goyon bayan na Atiku.

Daya daga cikin shugabanin matasan jam'iyyun siyasa ya mayar da martani a kan sakon gayyatar mawara Atiku baya da aka aike masa inda ya ce, "Na gode da gayyata sai dai ina son inyi karin haske domin CONYLOP ta kunshi jam'iyyun APC, ANN, AAC, ANRP, YPP, KOWA kuma kana nufin dukkan su suna goyon bayan Atiku? Muna jiran amsar ka."

A yayin da ya ke magana a madadin Jam'iyyar ANN, Direkta Janar na yakin zaben shugabancin kasa na jam'iyyar, Lanre Oyegbola ya ce ya amsa sakon da aka aike masa kamar haka: "Muna godiya da sako, sai dai muna son mu fayyace maka cewa ANN ba ta cikin jam'iyyun da ke goyon bayan Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, muna na da dan takarar shugaban kasa mai suna Mr Fela Durotoye, mun gode."

Ana sa ran za a sanar da jam'iyyun da ke goyon bayan Atiku ne misalin karfe 4 na yammacin yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel