Kungiya Ta Taso da Batun Takardun Karatun Tinubu, Ta Aika Wasika ga INEC

Kungiya Ta Taso da Batun Takardun Karatun Tinubu, Ta Aika Wasika ga INEC

  • An sake taso da batun takardun karatun Shugaba Bola Tinubu da aka yi ta takaddama a kai gabanin zaben shekarar 2023
  • Wata kungiya mai kare hakkin jama'a ta aika da wasika ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan batun takardun
  • Kungiyar ta bukaci hukumar INEC da ta ba ta karin haske kan shakkun da ake da shi kan takardun karatun shugaban kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Wata ƙungiyar kare haƙƙin jama'a, Center for Reform and Public Advocacy (CFRPA), ta aike da wasiƙa zuwa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), kan Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar tana neman ƙarin haske kan batutuwan da suka shafi takardun shaidar karatu da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Kara karanta wannan

An jibge jami'an tsaro, sun hana mutane zirga zirga a kananan hukumomi 2 a jihar Kano

An rubuta wasika zuwa ga INEC kan Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar Independent ta kawo rahoton cewa wasikar na dauke da kwanan 19 ga watan Yunin 2026.

Kungiyar ta aika da wasikar ne ga shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan.

Wace bukata aka nema wajen INEC?

A cikin wasikar, ƙungiyar ta ce tana neman bayani na shari'a ne kan abubuwan da ka iya biyo baya dangane da tambayoyin da ta tayar game da bayanan karatu na shugaban kasar da kuma yiwuwar tasirinsu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Wasiƙar, wadda shugaban sashen shari'a na ƙungiyar, Kalu Agu ya sanya wa hannu, an karɓe ta ne a hedkwatar INEC da ke Abuja a ranar da aka aika da ita.

A cewar ƙungiyar, buƙatarta tana da nufin haɓaka gaskiya da amincewar jama'a ga tsarin zaɓe gabanin babban zaɓe mai zuwa, rahoton Daily Post ya nuna hakan.

Kungiya na son bayanai kan takardun Tinubu

CFRPA ta yi iƙirarin cewa wasu bayanai da ke ƙunshe cikin bayanan da jami'ar jihar Chicago ta fitar da sauran takardu sun tayar da tambayoyin da, a ra'ayinta, ke buƙatar ƙarin haske daga hukumar zaɓe.

Kara karanta wannan

'Yan takara 6 mafi yawan shekaru da za su fafata a zaben gwamnan Ekiti

Ƙungiyar ta kuma yi nuni da tanade-tanaden tsarin mulki da suka shafi cancantar 'yan takara masu neman muƙaman zaɓe.

Ana son samun bayanai kan takardun karatun Shugaba Tinubu
Shugaban kasar Najeiya, Bola Ahned Tinubu Hoto:@aonanuga1956
Source: Facebook

Hakazalika ta buƙaci INEC da ta bayyana matsayinta na shari'a a fili game da batutuwan da ta tayar, tana mai cewa irin wannan ƙarin haske zai taimaka wajen magance damuwar da ake da ita game da buƙatun cancanta ga 'yan takara a zaɓubbuka masu zuwa.

CFRPA ta ƙara da cewa tana iya neman fassarar shari'a daga kotu kan tanade-tanaden tsarin mulkin da suka dace idan har hukumar zaɓen ba ta mayar da martani ga buƙatarta ta ba.

Tinubu ya taya Oyebanji murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu, ya taya Gwamna Biodun Abayomi Oyebanji, murnar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Mai girma Shugaba Bola Tinubu ya kuma yabawa al’ummar Ekiti bisa yadda suka gudanar da zaben cikin lumana da tsari.

Shugaban kasar ya ce yadda jama’ar jihar suka sake ba Oyebanji dama ya nuna sun amince da salon mulkinsa da ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a wa’adin farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com