Abin Mamaki: 'Yan Ta'adda Sun Tara Mutanen Gari, Sun Yi Masu Wa'azi a Jihar Neja
- Wasu ‘yan ta'adda masu ikirarin jihadi sun shiga Neja tare da tara mazauna Zugurma domin gabatar da wani wa’azi mai cike da barazana
- Mazauna yankin Zugurma sun ce mayakan sun iso garin da babura kusan 30 sanye da kayan sojoji da rawani kafin su rarraba kansu
- Ana zargin cewa 'yan ta'addar suna karkashin ƙungiyar Lakurawa ne, wacce masu nazarin tsaro ke danganta ta da ƙungiyoyin jihadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Neja - Wasu ‘yan ta'adda ɗauke da makamai sun shiga Zugurma, wani gari da ke jihar Neja kusa da gandun dajin Kainji Lake National Park.
An ce sun tara mazauna yankin tare da yi musu wa’azi mai ɗauke da barazana ga ɓarayi, masu shan taba da wasu makiyaya Fulani, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Source: Getty Images
'Yan ta'adda sun yi wa'azi a kauyen Neja
Majiyoyi da suka haɗa da shaidu sun bayyana wa Premium Times cewa mutanen da ke sanye da kayan sojoji da rawani sun isa yankin ne da kusan babura 30 da misalin ƙarfe 3:00 na rana.
Jaridar ta tattauna da wasu mutane biyar mazauna Zugurma, amma ba a bayyana sunayensu ba saboda dalilan tsaro.
Duk da cewa ba a tabbatar da asalin ƙungiyar ba, mazauna yankin da masu nazarin harkokin tsaro sun yi imanin cewa mayakan na cikin ƙungiyar Lakurawa.
Wasu masu bincike sun danganta ƙungiyar da cibiyoyin da ke da alaƙa da al-Qaeda, yayin da wasu suka gano alaƙa tsakaninta da ISSP, wadda a baya ake kira ISGS.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa akwai ƙungiyoyin jihadi da dama da ke aiki a yankin dajin Kainji. Bisa bayanan shaidu da hotunan da aka duba, tufafin mayakan da suka shiga Zugurma sun fi kama da na Lakurawa da Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda ke da alaƙa da al-Qaeda a yankin Sahel.
Wani mazaunin yankin ya ce ya fara haɗuwa da mayakan ne kusa da gadar da ta haɗa Hayin Kambari da Hayin Hausawa.
“Na so in ɗauki bidiyo nasu, amma ban samu damar yin hakan ba saboda ina kan babur,” in ji shi.
'Yan ta'adda sun tara mutane a masallaci
Wani shugaban al’umma ya ce wasu mazauna yankin sun gudu bayan ganin 'yan ta'addan, amma daga baya suka dawo bayan an gaya musu kada su gudu.
“Sun ce sun zo ne domin yi wa mutane wa’azi kawai,” in ji shugaban.
Mazauna garin da suka halarci wa’azin sun ce an gudanar da shi ne a wani ƙaramin masallaci da ke titin Mallam Dugu a Hayin Kambari.
Wani mai sayar da kayan masarufi ya ce mayakan sun iso yankin da babura 14, inda kowanne babur ke ɗauke da mutane biyu, sai guda ɗaya da ke ɗauke da mutum ɗaya da bindiga mai nauyi.
“Mutum ɗaya ne kawai ya shiga masallacin, sauran kuma suka tsaya a waje tare da mu,” in ji shi.

Source: Original
Wa'azin da 'yan ta'adda suka yi a Neja
A cewar mazauna yankin, mai wa’azin ya yi magana kan rashin imani, shan taba, sata da kuma rikicin manoma da makiyaya da ya dade yana faruwa, in ji rahoton Daily Nigerian.
Sun ce ya zargi wasu makiyaya Fulani da shiga gonaki ba tare da izini ba tare da lalata amfanin gona.
“Ya ce za su shiga tsakani idan makiyaya suka lalata amfanin gonakin manoma,” a cewar wani mazaunin yankin.
Mai wa’azin ya kuma yi barazana ga masu aikata laifuffuka, inda ya ce ƙungiyarsu za ta hukunta ko kashe ɓarayi, sannan za a yi wa masu shan taba bulala.
Mutanen garin ce an kwashe kusan mintuna 40 ana wa’azin, kuma wasu daga cikin waɗanda suka halarta sun riƙa tafa masa.
'Yan bindiga sun sanya harajin wa'azi
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun saka harajin yin wa'azi kafin barin malaman addini su yi karatu a wasu sassan jihar Kebbi.
Hakan na zuwa ne bayan mummunan hari da 'yan ta'adda suka kai jihar Kwara suka kashe rayuka sama da 100 bayan aika wa da wasikar gargadi.
Wata majiya ta ce mutanen garin da aka kakaba wa harajin sun shiga damuwa yayin da aka kara tura dakarun sojoji yankin da aka aika wasikar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


