Shiyyar Neja ta Gabas: INEC ta karbe tikitin takarar Sanata Umaru ta bai wa Sani Musa

Shiyyar Neja ta Gabas: INEC ta karbe tikitin takarar Sanata Umaru ta bai wa Sani Musa

- 2019: 'Dan Majalisar Neja ta Gabas ya rasa tutar APC yayin da ake shirin zabe

- Wani Sanatan APC a jihar Neja ya rasa tikitin jam'iyya ana daf da zabe

- Hukumar zabe ta kasa INEC ta karbe tikitin Sanata Umaru ta ba Sani Musa

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC reshen jihar Neja, ta karbe tikitin takarar kujerar wakilin shiyyar Neja ta Gabas na majalisar dattawa daga hannu Sanata David Umaru ta kuma danka shi a hannun Muhammad Sani Musa.

Shugaban INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu

Shugaban INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu
Source: Depositphotos

Sauya sunan dan takarar da hukumar INEC ta yi ya biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya, da ta tabbatar da Sani Musa a matsayin wanda ya yi nasarar samun tikitin takara a zaben fidda gwani da aka gudanar yayin da babban zaben kasa ke kan gaba.

Sakamakon hukuncin babbar kotun ya sanya hukumar zabe ta aike da wasika a ranar 15 ga watan Fabrairun 2019 zuwa kwamishinan hukumar reshen jihar Neja, Farfesa Sam Egu, inda ta umarce shi akan sauya sunan Sanata Umaru da na Sani Musa a matsayi marikin tutar APC.

KARANTA KUMA: Waiwaye: Furucin Buhari bayan dage zaben 2015

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, sabon dan takarar kujerar Sanatan Neja ta Gabas, Sani Musa, na daya daga cikin wadanda suka yiwa hukumar INEC kwangila ta samar da na'urar tantance masu kada kuri'a.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel