Siyasar Pantami Ta Kara Karfi a Gombe da Tsohon Hadimin Gwamna Ya Koma PDP
- Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe ta kara karfi bayan wani tsohon hadimin Gwamna Muhammadu Inuwa ya sauya sheka zuwa cikinta
- Aliyu Musa ya sanar da murabus dinsa daga APC zuwa jam'iyyar PDP inda aka karbe shi zuwa cikinta a hukumance
- Tsohon hadimin gwamnan ya bayyana shirinsa na ba da goyon baya ga takarar tsohon Ministan sadarwa da tattalin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Wani tsohon mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Gombe, Aliyu Musa, ya yi murabus daga jam'iyyar APC mai mulki inda ya koma PDP.
Aliyu Musa ya koma jam'iyyar PDP ne tare da dubban magoya bayansa, a wani mataki da zai ƙara sauya yanayin siyasa gabanin zaɓen gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Aliyu Musa ya sanar da sauya sheƙar tasa ne a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026 a lokacin wani taron da ƙungiyar "Awareness and Unity Programme" ta shirya a Ƙaramar Hukumar Billiri.
PDP ta samu karuwa a jihar Gombe
A wajen taron, shugaban jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Billiri ya mika masa tutar jam'iyyar a hukumance, kamar yadda Abba Sani Pantami ya sanya a Facebook.
Tsohon hadimin gwamnan ya ce shawararsa ta barin APC ta samo asali ne daga goyon bayan da yake ba wa burin takarar gwamna na tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, a watan Mayun 2025, ya naɗa Musa tare da wasu mutane 15 a matsayin hadiminsa, inda ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman II kan harkokin siyasa.
Takarar Isa Pantami ta samu karuwa
A cewar masu shirya taron, fiye da maza da mata 1,800 daga karamar hukumar Billiri su ma sun fita daga APC da Jam'iyyar Labour (LP) domin komawa PDP don nuna goyon baya ga takarar gwamna ta Pantami.
Magoya bayan sun jaddada cewa ana sa ran waɗannan sauya sheƙa na baya-bayan nan za su ƙarfafa PDP a tsakanin talakawan karkara a mazabar sanatan Gombe ta Kudu musamman a Billiri.

Source: Facebook
Pantami zai yi takarar gwamna a Gombe
Pantami, wanda ya bar APC sakamakon rashin jituwa kan tsarin zaɓen fitar da gwani na gwamna na jam'iyyar, an tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na PDP a watan Mayun 2026.
Ya yi alƙawarin gudanar da gwamnati ta bai-ɗaya da za ta mayar da hankali kan rage talauci, ilimi, noma, da kuma masana'antu idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna.
Jam'iyyar PDP ta samu nasara a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta samu nasara a zaben cike gurbi na mazabar sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar PDP, Olaka Nwogu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas.
An gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin marigayi Sanata Barry Mpigi, wanda ya rasu a watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki ta 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

