Zaben Gwamna Ekiti: APC Ta Aika Sako ga Oyebanji bayan Samun Tazarce

Zaben Gwamna Ekiti: APC Ta Aika Sako ga Oyebanji bayan Samun Tazarce

  • Gwamna Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026
  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta taya gwamnan murna kan nasarar da ya samu a zaben wanda ya ba abokan hamayyarsa tazara mai nisa
  • APC ta jinjinawa hukumar zabe ta INEC ta sauran masu ruwa da zaki saboda namijin kokarin da suka yi wajen gudanar da zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta aika da sakon taya murna ga gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.

Jam'iyyar APC ta taya Biodun Oyebanji murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Ekiti na ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Oyebanji ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti
Gwamna Biodun Oyebanji a wajen yakin neman zabe Hoto: Biodun Oyebanji
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na APC na kasa, Felix Morka, ya sanya a shafin X a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Cikakken sakamakon zaben gwamnan Ekiti kamar yadda INEC ta sanar

APC ta ce Oyebanji ya kafa tarihi

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa nasarar Biodun Oyebanji cike take da tarihi, domin ya zama gwamnan farko da ya yi tazarce a jihar Ekiti.

"Jam'iyyar APC tana taya Mai girma Gwamna, Biodun Abayomi Oyebanji, murnar sake zabensa da aka yi a matsayin gwamnan jihar Ekiti."
"Nasarar Gwamna Oyebanji abu ne mai cike da tarihi, domin shi ne gwamna mai ci na farko da ya taba yin tazarce ta hanyar sake lashe zabe a tarihin dimokuradiyyar jihar."
"Wannan nasara babbar shaida ce da ke nuna amincewar mutanen Ekiti ga Gwamna Oyebanji, da jajirtaccen jagorancinsa, da manufofinsa da suka mayar da hankali kan jin dadin jama'a, da kuma sadaukarwarsa ga ci gaban jihar."

- Felix Morka

APC ta yabawa hukumar INEC

Jam'iyyar APC ta kuma jinjinawa hukumar zabe ta INEC, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki saboda kokarin da suka yi a lokacin zaben.

"Muna jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), hukumomin tsaro, da daukacin masu ruwa da tsaki wadanda kokarinsu da kwarewarsu suka ba da gudunmawa wajen gudanar da zaben cikin nasara."

Kara karanta wannan

Bayan fafatawar APC da PDP, ADC, INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben Ekiti

"Jam'iyyar tana yaba wa al'ummar Jihar Ekiti saboda halayensu na zaman lafiya da kuma shiga harkar zaben da suka yi da matukar karsashi a duk lokacin gudanar da zabuka."
"Muna ci gaba da kasancewa masu matukar godiya saboda tsayin daka da goyon bayansu, da kuma amincewa da babbar jam'iyyarmu, da manufofinta, da kuma kyawawan akidojinta na ci gaba."
"Muna da yakinin cewa wa'adin mulki na biyu na Gwamna Oyebanji zai kawo karin ci gaba da ingantacciyar rayuwa ga jama'a yayin da yake fadada ayyukan manufar 'Renewed Hope' ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin jihar."

- Felix Morka

APC ta taya Oyebanji murnar lashe zabe
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

An kona ofishin 'yan sanda a zaben Ekiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi Allah-wadai da kona wani ofishin ‘yan sanda da aka yi a garinsu.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne garinsu na Isan-Ekiti, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Fayemi bayan ya kammala kada kuri'arsa, ya bayyana cewa lamarin ba shi da wata alaƙa da zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng