Ban da buri a siyasa da ya wuci in ga ‘Dan Talaka ya zama wani iri na – Atiku

Ban da buri a siyasa da ya wuci in ga ‘Dan Talaka ya zama wani iri na – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma ‘dan takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya fadi dalilin sa na shiga cikin harkar siyasa.

Ban da buri a siyasa da ya wuci in ga ‘Dan Talaka ya zama wani iri na – Atiku
'Dan takarar PDP Atiku ya fadi burin da ya ke da shi a siyasa
Asali: Facebook

A wata hira da Atiku Abubakar yayi kwanaki wanda ya shigo hannun mu, an tambaye sa game da babban burin da yake da ita a siyasa. Atiku ya fara siyasa a Najeriya ne tun a lokacin mulkin Sojan Janar Ibrahim Babangida.

‘Dan takarar yake cewa bai da buri da ya wuce ya ga yaron Talaka wanda ba ‘dan kowa bane ya zama ya samu gata a cikin kasar nan. Atiku dai yake cewa abin da yake so shi ne ya ga irin sa wanda ba ‘dan kowa ba ya zama wani.

KU KARANTA: Ina na nan a kan baka ta na sayar da kamfanin NNPC - Atiku

Atiku ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jaridar DW na kasar Jamus. Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya yana cewa yadda ya tashi ya har ya zama wani, yana da burin ya ga wasu sun zama haka.

Alhaji Atiku Abubakar dai yana ikirarin cewa iyayen sa ba Attajirai bane, amma ya tashi ya samu ilmin boko har ya samu abin yi, ya kuma kafa kan sa. Yanzu haka babban ‘dan siyasar yana cikin manyan Attajiran kasar nan.

Mai neman shugaban kasar a karkashin PDP yake cewa yana da sha’awar ganin Yara sun tashi sun samu karatun zamani sun zama mutane masu zaman kan-su wadanda za su yi duk irin aikin da su ke sha’awa a rayuwar su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel