Ba saboda dalilai na siyasa na yi ritaya ba - Sani Kukasheka

Ba saboda dalilai na siyasa na yi ritaya ba - Sani Kukasheka

- Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (rtd), ya yi watsi da rade-radin da ke yaduwa kan cewa ya ajiye aikin soja saboda wasu dalilai na siyasa

- Tsohon Kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya ya ce ba bu kamshin gaskiya dangane da rade-radin da ke yaduwa a kasar nan

- Kukasheka ya ce ba zai gushe ba wajen ci gaba da godiya ga hukumar sojin kasa ta Najeriya da ta ba shi damar yiwa kasar sa hidima

Tsohon kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, ya yi karin haske na tabbatar da dalilai da suka sanya ya ajiye aikin sa na damara a karkashin hukumar dakarun sojin kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Birgediya Janar Kukasheka ya yi wasti da rade-radin da ke yaduwa a kafofin sadarwa na kasar da nunin da cewa ya ajiye aikin sa sakamakon wasu dalilai da akidu na siyasa.

Ba saboda dalilai na siyasa na yi ritaya ba - Sani Kukasheka
Ba saboda dalilai na siyasa na yi ritaya ba - Sani Kukasheka
Asali: Facebook

A yayin karyata wannan rahoto da ya misalta shi da mafi kololuwar rashin gaskiya, Kukasheka ya ce ba zai gushe ba wajen ci gaba da godiya ga hukumar sojin kasa ta Najeriya da ta ba shi damar yiwa kasar sa hidima.

A cewar Janar Kukasheka, ya ce ba bu wasu dalilai da suka sanya ya ajiye aikin sa na damara bayan ya shafe fiye da tsawon shekaru talatin face dalilai na haka siddan bisa ga madogara ta ra'ayi na karan kansa.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Atiku ya gudanar da zaman sauraron ra'ayi a jihar Kaduna

Shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito cewa, Birgediya Janar Kukasheka ya yi ritaya daga aikin soja a ranar 7 ga watan Fabrairun 2019, bayan ya shafe tsawon shekaru talatin ya na yiwa kasar sa hidima.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel