'Za Ta Karewa Tinubu a 2027,' Momodu Ya Fadi Yadda Atiku zai Kifar da APC

'Za Ta Karewa Tinubu a 2027,' Momodu Ya Fadi Yadda Atiku zai Kifar da APC

  • Fitaccen dan siyasa a Kudanci Najeriya, Dele Momodu ya ce zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 zai yi wa shugaba Bola Tinubu wuya sosai
  • Momodu da ke ADC ya bayyana cewa Atiku Abubakar zai iya lashe mafi yawan ƙuri’un Arewa tare da samun kaso mai tsoka a Kudancin kasar nan
  • Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyun siyasa da 'yan takarar da aka tsayar ke cigaba da tattaunawa da al'umma domin neman goyon bayansu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya yi hasashen cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 zai kasance mai tsanani ga Shugaba Bola Tinubu.

Hakan na zuwa ne yayin da Atiku Abubakar da jam'iyyar ADC suka zabi Rotimi Amaechi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sojoji za su fara shiga daji yaki da 'yan bindiga tare da 'yan jarida

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu, Atiku Abubakar a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Paul Ibe
Source: Facebook

Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da ɗan jarida Oseni Rufai a kafar Nevon Media ranar Juma’a, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, zai yi nasara.

'Atiku zai yi nasara a 2027,' Momodu

A cewar Momodu, Atiku na iya kayar da Tinubu da kuma ɗan takarar NDC, Peter Obi, idan ya samu cikakken goyon baya a Arewacin Najeriya tare da samun kuri'u sosai a Kudu.

“Kamar yadda na yi hasashe, Atiku zai lashe mafi yawan ƙuri’un Arewacin Najeriya, kuma idan ya nuna bajinta yadda ya kamata a Kudancin Najeriya, to komai zai ƙare wa shugaba Tinubu da Peter Obi,”

In ji shi.

Punch ta wallafa cewa Momodu ya kara da cewa:

“Atiku zai samu aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a jihohi 26, tare da mamaye Arewacin Najeriya, wanda shi ne yankin da ke da mafi yawan ƙuri’u,”

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da za su iya sanya APC lashe zaben gwamnan Ekiti na 2026

Dele Momodu a wajen taro
Dele Momodu yana wani jawabi. Hoto: Dele Momodu
Source: Twitter

Magana kan tsarin mulkin kasa

Momodu ya yi nuni da tanade-tanaden kundin tsarin mulki kan lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda ya ce dole ne ɗan takara ya samu mafi yawan ƙuri’un ƙasa baki ɗaya tare da samun aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a jihohi biyu bisa uku na ƙasar.

Ya nuna tabbacin cewa Atiku zai iya cika wannan sharadi ta hanyar haɗa kan magoya baya a jihohin Arewa masu yawan masu kaɗa ƙuri’a.

Ya ce:

“Da zarar ka samu dimbin ƙuri’u daga Arewa, hakan zai rage karfin Kudancin Najeriya. Wannan ne ya sa Tinubu ke kokarin ganin an soke wasu jam’iyyu. Musamman saboda Atiku.
"Kuma Arewa ta riga ta ɗauki mataki mai muhimmanci a wannan karon. Wannan matakin yana da matuƙar muhimmanci domin sun tabbatar babu wani babban jagora daga Arewa da zai yi takara da Atiku."

Ana zabe a Kano da jihohi

A wani labarin, mun kawo muku cewa a yau Asabar, 20 ga watan Yunin 2026 ake gudanar da zabuka a wasu jihohin Najeriya shida.

Kara karanta wannan

Zaben fitar da gwani: APC ta yi martani bayan tsohon sufeta janar ya fice daga cikinta

Za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti, inda gwamna mai ci ke jam'iyyar APC mai mulki kuma ya ke neman wa'adi na biyu.

Haka zalika zaben zai gudana a wasu jihohi da suka hada da Kano, Enugu, Nasarawa, Rivers domin maye gurbin wadanda suka rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng