"Firaministan Birtaniya Zai Yi Murabus," Donald Trump Ya Yi Magana kan Keir Starmer

"Firaministan Birtaniya Zai Yi Murabus," Donald Trump Ya Yi Magana kan Keir Starmer

  • Donald Trump ya ce Firaministan Birtaniya Keir Starmer zai yi murabus saboda gazawa kan batutuwan shige da fice da makamashi
  • Shugaban Amurka ya soki manufofin Firaminista Starmer, yayin da ake samun rade-radin matsin lamba daga wasu ‘yan jam’iyyar Labour
  • Rahotanni sun ce wasu ministoci na matsa wa Starmer lamba ya tsara lokacin mika mulki bayan rikicin cikin gida da ya dabaibaye London

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer, na dab da yin murabus daga mukaminsa.

Donald Trump ya yi wannan furucin ne bayan ya yi zargin cewa Starmer ya gaza wajen magance matsalolin shige da fice da kuma makamashi.

Trump ya yi hasashen murabus din firaministan Birtaniya, Keir Starmer.
"Firaministan Birtaniya, Keir Starmer tare da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Firaminista zai yi murabus' - Trump

Trump ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Truth Social, inda ya ce Starmer ya gaza a wasu muhimman batutuwa biyu da suka hada da shige da fice da kuma harkar makamashi.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano

“Keir Starmer zai yi murabus a matsayin Firayim Ministan Birtaniya. Ya gaza sosai a kan muhimman batutuwa biyu — Shige da fice da makamashi,” in ji Trump.

Wannan ba shi ne karo na farko da Trump ke bayyana rashin gamsuwa da manufofin gwamnatin Starmer ba.

A cikin watannin baya, shugaban Amurka ya sha yin kira ga Firaministan Birtaniya da ya dauki tsauraran matakai kan kula da iyakokin kasar domin rage yawan masu shigowa ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma Trump ya bukaci Birtaniya ta kara amfani da albarkatun man fetur da iskar gas da ke yankin Tekun Arewa, yana sukar matakan da gwamnati ke dauka kan makamashi.

A watan da ya gabata, Trump ya ce zai yi wahala Starmer ya tsira daga matsin lambar siyasa bayan mummunan sakamakon da jam’iyyar Labour ta samu a zabukan kananan hukumomi.

Rade-radin sauyin shugabanci a Birtaniya

Rahotanni daga Birtaniya sun nuna cewa Starmer na fuskantar matsin lamba daga wasu bangarorin jam’iyyarsa, inda ake hasashen yiwuwar samun sauyin shugabanci.

Wasu na ganin nasarar Andy Burnham a wani zaben cike gurbi ta kara karfafa rade-radin cewa akwai bukatar sabon jagoranci a Labour, kamar yadda Financial Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Bai da kwarewa": Babban sanata a Amurka ya soki Trump saboda yarjejeniyar Iran

Ana sa ran wasu abokan siyasar Starmer na iya goyon bayan wani tsarin mika mulki cikin sauki idan har ya yanke shawarar barin ofis.

Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da matsin lamba ga Keir Starmer ya mika mulki
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya na magana da 'yan jarida bayan taron G7. Hoto: Isabel Infantes - WPA Pool/Getty Images
Source: Getty Images

Ministoci sun fara matsa lamba

Rahotanni sun ce wasu manyan jami’an gwamnati ciki har da ministan harkokin wajen Birtaniya, Yvette Cooper, da sauran ministoci sun fara nuna bukatar a fayyace makomar jagorancin kasar.

An bayyana cewa Starmer ya shafe kwanaki yana tattaunawa da ministoci, abokansa da kuma matarsa, Victoria, kan matakin da zai dauka.

Wasu na ganin idan har ya sauka daga mulki, hakan zai iya bude hanyar da Andy Burnham ya zama sabon shugaban kasar Birtaniya.

Rigimar Trump da Starmer a yakin Iran

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sir Keir Starmer ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta shiga cikin shirin Amurka na killace tashoshin jiragen ruwan Iran ta hanyar amfani da dakarun soji ba.

Ko da yake Birtaniya za ta ci gaba da amfani da na'urorin daƙile jirage marasa matuƙi a yankin, Starmer ya ce ba za a yi amfani da jiragen yaƙi ko sojojin Birtaniya wajen toshe hanyoyin ruwan Iran ba.

Wannan takun-saƙa ya biyo bayan sanarwar da Shugaba Donald Trump ya yi, inda ya bayyana cewa Amurka za ta fara toshe dukkan jiragen ruwan da ke ƙoƙarin shiga ko fita daga tashoshin Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com