Esposito: Babban Jarumin Fim a Amurka Ya Karbi Addinin Musulunci a Saudiyya

Esposito: Babban Jarumin Fim a Amurka Ya Karbi Addinin Musulunci a Saudiyya

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa fitaccen jarumin fim din kasar Amurka, Giancarlo Esposito ya karbi addinin Musulunci yayin da ya je aiki Saudiyya
  • Bayanan da suka fito daga Saudiyya sun nuna cewa jarumin ya furta kalmar shahada tare da yin sallah a wani masallaci yayin ɗaukar fim
  • Jami'in kasar Saudiyya, Turki Al-Sheikh ya bayyana cewa kyakkyawar hulɗarsa da Musulmai yayin da yake aiki ta taimaka wajen shiga Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudiyya - Jarumin fim din Amurka, Giancarlo Esposito, wanda aka fi sani da rawar Gus Fring da ya taka a shirin talabijin na Breaking Bad, ya shiga Musulunci.

Giancarlo Esposito ya karbi addinin Musulunci ne yayin da yake kasar Saudiyya, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai suka bayyana a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Trump, Firaministan Birtaniya ya sauka daga mukaminsa

Dan fim, Giancarlo Esposito
Giancarlo Esposito a wani waje a kasar Masar. Hoto: Giancarlo Esposito
Source: Facebook

Jarumin fim ya shiga addinin Musulunci

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa shugaban hukumar nishaɗi ta kasar Saudiyya, Turki Al-Sheikh, ya ce Esposito ya furta kalamar shahada.

Bugu da kari, an ce jarumin ya yi sallah tare da wasu mambobin tawagar shirya fim a wani masallaci yayin da suke ɗaukar fim a Saudiyya.

A cewar Al-Sheikh, matakin da jarumin ya ɗauka ya biyo bayan kyawawan abubuwan da ya gani a lokacin zamansa a Saudiyya da kuma hulɗarsa da Musulmai yayin aikin wani fim da yake yi a ƙasar.

Jami'in kasar Saudiyya ya kara da cewa Esposito ya nuna godiya ga al'umma da kyakkyawar tarbar da ya samu yayin aikin ɗaukar fim ɗin.

Abin da ya sa jarumin shahara

Esposito ya shafe shekaru masu yawa yana taka rawa a fina-finai da shirye-shiryen talabijin, kuma an san shi da rawar da ya taka a Better Call Saul, The Mandalorian da sauran shirye-shirye.

Kara karanta wannan

"Yan hassada ne": Trump ya hasala kan masu sukar yarjejeniyar Amurka da Iran

Rahoton ya ce ya samu karɓuwa sosai a duniya tare da samun guraben lambar yabo da dama saboda yadda ya fito a matsayin Gus Fring.

Giancarlo Esposito yana dariya
Giancarlo Esposito da ya karbi addinin Musulunci. Hoto: Giancarlo Esposito
Source: Facebook

Bayani game da jarumin

Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa Giancarlo Esposito fitaccen jarumi ne da ya yi suna a duniya, wanda ya shafe shekaru masu yawa yana harkar fim.

An fi saninsa da rawar da ya taka a shahararrun shirye-shiryen talabijin irin su Breaking Bad, Better Call Saul da The Boys.

Haka kuma ya taka rawa a fina-finai da shirye-shiryen talabijin kamar The Mandalorian, Do the Right Thing da Godfather of Harlem.

An fi saninsa da taka rawar rin ta mutane mugaye a fina-finai, inda yake gabatar da su cikin sauƙi, tsoro da kuma ƙwarewa.

'Yar fim ta magantu kan aure

A wani labarin, kun ji cewa jarumar fim din Hausa, Nafisat Abdullahi ta bayyana cewa babu aure a cikin abubuwan da ta saka a gaba.

Jarumar ta bayyana cewa yawanci maza na aure ne domin su samu wacce za ta rika yi masu bauta amma ita ba za ta iya haka ba sam-sam.

Nafisat ta yi kira ga mata da su dage wajen gina kan su ta hanyar sana'o'i da neman kudi domin samun daukar nauyin bukatunsu na rayuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng