Osinbajo ya daura damarar warware rikicin APC a jihar Zamfara

Osinbajo ya daura damarar warware rikicin APC a jihar Zamfara

- Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya shiga tsakanin rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara

- Osinbajo ya gana da Sanata Kabiru Marafa a fadar Villa domin warware rikicin APC a jihar Zamfara

- Sanata Marafa ya ce dage babban zaben kasa zai bayar da dama ga jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta kawo karshen rikicin ta

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya daura damara ta shiga tsakani domin warware rikicin da ya mamaye jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara.

Sanata Kabiru Marafa
Sanata Kabiru Marafa
Asali: Twitter

Kamar yadda Sanata Kabiru Marafa ya bayyana, mataimakin shugaban kasar ya shimfida wasu shawarwari na kawo karshen rikicin da ya mamaye jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara tare da yi ma ta katutu.

Sanata Marafa ya bayar da shaidar hakan ne cikin wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa a yau Talata bayan ganawar sa da mataimakin shugaban kasar dangane da dambarwa ta rikicin da ya hana ruwa gudu a jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara.

Wakilin shiyyar Zamfara ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan kasar nan ya kuma bayyana cewa, dage babban zaben kasa da hukumar INEC ta yi zai bayar da dama domin jam'iyyar APC ta sulhunta rikicin da ya yi ma ta kaka-gida a jihar Zamfara.

KARANTA KUMA: Dage babban zaben Najeriya laifin Buhari ne - Sanatan Amurka, Chris Smith

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi haramci na tsayar da kowane dan takara a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara sakamakon dambarwa ta rikici da ya biyo bayan zaben ta na fidda gwanayen takara.

Yayin ci gaba da ganawa da manema labarai, Sanata Marafa ya ce ya ziyarci fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa gayyatar Farfesa Osinbajo domin shawo kan matsalar jam'iyyar su ta APC reshen jihar Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel