Hotuna: Jiragen sama na gwamnatin jihar Akwa Ibom sun iso birnin Uyo

Hotuna: Jiragen sama na gwamnatin jihar Akwa Ibom sun iso birnin Uyo

Mun samu cewa, a yayin da gwamnatin jihar Akwa Ibom karkashin jagorancin gwamna Udom Emmanuel ta daura damarar samar da kamfanin jiragen sama na karan kanta, a yau Laraba tsala-tsalan jiragen sama biyu sun dira a birnin Uyo.

Ibom Air ya dira a birnin Uyo

Ibom Air ya dira a birnin Uyo
Source: Twitter

Jiragen sama na gwamnatin jihar Akwa Ibom sun iso birnin Uyo

Jiragen sama na gwamnatin jihar Akwa Ibom sun iso birnin Uyo
Source: Twitter

Ibom Air yayin dirar su a birnin Uyo

Ibom Air yayin dirar su a birnin Uyo
Source: Twitter

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta mallaki jiragen sama

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta mallaki jiragen sama
Source: Twitter

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a yau Laraba da Hausawa ke ma ta kirari na Tabawa ranar samu, wasu sabbin jiragen sama biyu sun dira a birnin Uyo domin kaddamar da aikin jigila kamar yadda gwamnatin jihar Akwa Ibom ta kudirta.

KARANTA KUMA: 2019: Shugaban kasa Buhari ne zabin mu - Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, shine zai jagoranci bikin kaddamar da wannan katafare na ci gaban kasa da kowace gwamnati za ta yi sha'awa wajen habaka tattalin arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel