Rundunar Sojan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin Buhari akan barayin akwatin zabe

Rundunar Sojan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin Buhari akan barayin akwatin zabe

Rundunar Sojan kasan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari daya bayar na bindige duk wani ko wasu da aka kama suna kokarin sace akwatin zabe a babban zaben kasar da zai gudana a mako mai zuwa.

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya bada wannan umarni yayin wani taron jam’iyyar APC na musamman daya gudana a babban ofishin jam’iyyar na kasa dake babban birnin tarayya a Abuja, sai dai batun ya janyo cecekuce a tsakanin yan Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna da Bankin duniya zasu gina babban kamfanin sarrafa citta

Rundunar Sojan Najeriya ta dauki alwashin cika umarnin Buhari akan barayin akwatin zabe
Buhari da Buratai
Asali: Facebook

Yayin da wasu ke ganin wannan mataki na shugaban kasa yayi daidai, wasu kuma na ganin matakin yayi tsauri dayawa, a cewarsu ba’a hukunta barawon akwatin zabe da bindiga, daga cikin wadanda suka koka kan umarnin na Buhari akwai jam’iyyar PDP, Sanata Shehu Sani, Yakubu Dogara da sauransu.

Sai dai da take tsokaci game da wannan umarni na shugaban kasa, rundunar Sojan kasa ta bayyana shirinta da kuma manufarta na dabbaka umarni ba tare da wata wata ba, matukar shugaban kasa ne ya bayar da ita.

“Idan har babban kwamandan askarawan Sojin Najeriya ne ya bayar da wannan umarni ga rundunar Sojan kasa, ku sani tabbas zamu aiwatar da wannan umarni gaba dayansa dari bisa dari ba tare da wani kwana kwana ba.” Inji Kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa.

Sai dai kafin wannan zance na shugaban kasa, rundunar Sojan kasa ta bayyana cewa zata jibge dakarunta a cikin shirin ko-ta-kwana amma ba’a kusa da akwatin zabe ba don gudun tsoratar da masu zabe, amma da wannan umarni, sai dai muyi kira ga masu shirin satan akwatin zabe dasu shiga taitayinsu.

A wani labarin kuma, wani kazamin karon battar dakarun Sojin Najeriya da mayakan Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda guda biyar, yayin da Sojoji suka yi asarar jami’ai guda hudu, daga cikinsu har da wani hafsan Soja.

Legit.ng ta ruwaito Kanal Sagir Musa ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fiyar a ranar Lahadi, 17 ga watan Feburairu, inda yace sun kashe yan ta’addan biyar a lokacin da suka yi kokarin tarwasa sansanin Sojojin da misalin karfe 6:5 na yammacin Asabar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel