Gwamnatin Tarayya Ta Fara Yunkurin Karya Farashin Buhun Siminti a Najeriya
- Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce Gwamnatin tarayya za ta fara tattaunawa da kamfanonin siminti daga ranar 1 ga Yuli domin rage tsadar siminti
- Umahi ya ce hauhawar farashin siminti na janyo matsin lamba ga ayyukan gine-ginen gwamnati da kuma bukatun karin kudin kwangila
- Ya bukaci kamfanonin su rage farashi tare da kara yawan samar da siminti domin biyan bukatun ayyukan more rayuwa da gwamnati ke gudanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta fara tattaunawa da kamfanonin siminti daga ranar 1 ga watan Yuli, 2026.
Ministan ya ce wannan tattauna za ta maida hankali ne kan duba yiwuwar magance matsalar tsadar siminti a fadin Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Umahi ya bayyana hakan ne a bikin kaddamar da sabon suna da tambarin kamfanin Lafarge, wanda yanzu ya koma HBM karkashin kungiyar HUAXIN Group.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Francis Nwaze, ya fitar a Abuja ranar Litinin, ministan ya nuna damuwa kan yadda farashin siminti ke ci gaba da tashi.
Ana so kamfanoni su rage tsadar siminti
Ministan ya ce hauhawar farashin siminti na kawo cikas ga ayyukan gine-ginen gwamnati tare da kara matsin lamba daga ‘yan kwangila da ke neman a kara musu kudaden aiki.
Umahi ya ce:
“Ina so in jaddada cewa kamfanin Lafarge da yanzu ya koma HBM, tare da sauran kamfanonin siminti, dole ne su rage farashin siminti. Za mu fara tattaunawa a kan wannan daga ranar 1 ga watan Yuli, 2026."
"Dole ne masu samar da siminti su rage farashi saboda ‘yan kwangila suna matsa mini lamba a duba kwangilolinsu. Amma ba za a sake duba kwangilar kowa ba, kamfanonin siminti ne ya kamata su rage kudinsu.”
Ya bukaci kara yawan samar da siminti
Umahi ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na zuba jari sosai a bangaren ayyukan more rayuwa a fadin kasar nan, lamarin da ya samar da sababbin damammaki ga masana’antu.

Kara karanta wannan
Matasan Arewa sun gano abin da ke kullawa domin sauke manyan hafsoshin tsaron Najeriya
Saboda haka, ya bukaci kamfanin HBM da sauran kamfanonin siminti su kara karfin samar da kayayyakinsu domin biyan bukatun ayyukan da ake gudanarwa.

Source: Facebook
Umahi ya yaba wa Kamfanin HBM
Ministan ya yaba wa kamfanin HBM kan sauya suna da kuma ci gaba da zuba jari a Najeriya, inda ya tabbatar musu da hadin kai da goyon bayan gwamnati, kamar yadda Leadership ta kawo.
Ya ce:
“Ina yaba muku sosai kuma ina maraba da ku, za mu yi aiki tare. Kasuwar da ake da ita yanzu ta fi karfin abin da ake samarwa, saboda haka ku fadada harkokinku.”
Farashin buhun siminti ya tashi
A wani labarin, kun ji cewa farashin buhun siminti ya tashi zuwa fiye da N10,500 a sassan Najeriya wanda hakan ya tsayar da ayyukan gine-gine da dama.
Binciken kasuwanni da aka gudanar a Kwara, Abuja, Kano, Kaduna, da Jigawa ya nuna cewa wannan ƙarin ya shafi kusan dukkanin manyan kamfanonin siminti na ƙasar nan.
Wannan tashin farashin ya sa ayyukan gine-gine da dama sun tsaya, yayin da masu yin bulo suka bayyana cewa kasuwancinsu na fuskantar barazana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
