Lionel Messi Ya Kere Ronaldo, Ya Kafa Sabon Tarihi a Gasar Cin Kofin Duniya

Lionel Messi Ya Kere Ronaldo, Ya Kafa Sabon Tarihi a Gasar Cin Kofin Duniya

  • Dan wasan gaba na kasar Argentina, Lionel Messi, ya kafa sabon tarihi a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake gudanarwa a kasashen Amurka, Mexico da Canada
  • Lionel Messi ya zuwa kwallo a wasan Argentina da Austria, wanda hakan ya sanya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a gasar cin kofin duniya
  • Dan wasan gaba na Faransa, Kylian Mbappe zai iya karya wannan tarihi na Messi idan ya ci gaba da zura kwallaye a gasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Amurka - Dan wasan gaba na kasar Lionel Messi ya zama wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihi a gasar cin kofin duniya.

Ɗan wasan mai shekaru 38 ya ci ƙwallonsa ta 17 a gasar kofin duniya a minti na 38 na wasan da Argentina ke bugawa da Austria a ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2026 domin kafa sabon tarihi.

Kara karanta wannan

World Cup 2026: Kasar Ghana ta karya tarihin Najeriya a gasar cin kofin duniya

Messi ya kafa tarihi a gasar cin kofin duniya
Lionel Messi na murnar zuwa kwallo a gasar cin kofin duniya Hoto: Charlotte Wilson
Source: Getty Images

Sanannen dan jarida mai kawo labaran kwallon kafa, Fabrizio Romano, ya sanar da hakan a shafinsa na X.

Messi ya kafa tarihi

A ƙarshe Messi ya tsallake Miroslav Klose na Jamus, wanda tarihin ƙwallayensa 16 ɗan wasan na Argentina ya kamo ta hanyar zura ƙwallaye uku rigis a wasansa na farko na kofin duniya na shekarar 2026 da suka buga da Algeria, TheCable ta kawo rahoton.

Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau takwas ya zura wannan ƙwallo ta tarihi ne ta hanyar salon nan nasa na zura kwallo, wanda hakan ya sa Argentina a gaba da Austria a wasansu na biyu.

Tun da farko a cikin wasan, Messi ya barar da kwallo lokacin ya buga bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka kawo katsalandan ga Lautaro Martinez a cikin akwatin Austria.

Wane dan wasa ne zai iya kamo Messi?

Ɗan wasa guda ɗaya tilo da zai iya yin ɗan barazana ga tarihin da Messi ya cimma shi ne Kylian Mbappé, wanda ke da ƙwallaye 14 a gasar cin kofin Duniya.

Kara karanta wannan

Bayan sulhu da Iran, Trump ya soki Netanyahu, ya zarge shi da babban laifi

Sauran sunaye da ke cikin jerin tarihin ko dai sun yi ritaya ko kuma sun rasu. Ronaldo Nazario na Brazil ya ci ƙwallaye 15 a Kofin duniya, sannan Gerd Müller na Jamus ya biyo baya da ƙwallaye 14. Marigayi babban ɗan wasa Pelé da Fontaine na Faransa ne ke biye da su a jerin.

Messi yana buga gasar kofin duniya ta shida ne, tarihin da ya kafa tare da Cristiano Ronaldo da kuma Guillermo Ochoa.

Messi ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya
Lionel Messi na murnar zura kwallo a wasan Argentina da Austria a gasar cin kofin duniya Hoto: Georg Hochmuth
Source: Getty Images

Ghana ta karya tarihin Najeriya a kofin duniya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar kungiyar kwallon kafa kasar Ghana ta karya tarihin da Super Eagles ta Najeriya ta kafa a gasar cin kofin duniya.

Nasarar da Ghana ta samu a wasanta da Panama, ya sa ta kai nasarori shida a tarihin wasannin da ta taka a kofin duniya, inda ta kamo Najeriya a matsayin kasashen Afirka da suka fi samun nasarori a gasar.

Ghana ta cimma wannan nasara a cikin wasanni 16 kacal, yayin da Najeriya ta samu nasarori shida bayan buga wasanni 21.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng