Gwamnatin Tarayya Ta Raba Buhunan Taki 100,800 ga Manoman Kano da Wasu Jihohi 4
- Hukumar NADF ta fara rabon buhunan taki 100,800 ga kananan manoma 25,200 a jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi da Jigawa
- Shirin tallafin takin na Renewed Hope (FISP) na da manufar rage kudin noma, kara amfanin gona da bunkasa samar da abinci Najeriya
- Hukumar NADF ta ce za ta tura fiye da jami’an wayar da kai kan noma 1,800 domin taimaka wa manoma da dabarun noma na zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Katsina - Hukumar Kula da Bunkasa Aikin Noma ta Kasa (NADF) ta fara rabon buhunan taki 100,800 ga kananan manoma 25,200 a jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi da Jigawa domin taimaka musu wajen bunkasa noma da kara samar da abinci.
Rabon takin na gudana ne karkashin shirin Renewed Hope - FISP wanda gwamnatin tarayya ta samar domin rage wahalhalun da manoma ke fuskanta wajen samun kayayyakin noma masu inganci.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An rushe katafaren gidan kasurgumin mai garkuwa da mutane da aka cafke a Edo

Source: Twitter
Kowane manomi zai samu buhu 4 na taki
Shugaban NADF, Mohammed Ibrahim, ya bayyana cewa shirin wani bangare ne na kokarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karfafa samar da abinci da inganta rayuwar manoma, in ji rahoton NAN.
Ya ce kowane manomi da aka zaba zai samu buhunan taki hudu kyauta.
A cewarsa, kowace jiha daga cikin jihohin biyar za ta samu buhunan taki 20,160, wadanda za a raba wa manoma 5,040 a kowace jiha.
Ya bayyana cewa an zabi manoman ne ta hanyar rassan jihohin kungiyar manoma ta kasa (AFAN).
An sanya alamar hana sayar da takin
Ibrahim ya ce an samar da takin da ake rabawa a cikin gida, kuma an sanya masa alamar “Ba na sayarwa ba ne” domin hana karkatar da shi ko sake sayar da shi a kasuwa.
Ya kara da cewa NADF na shirin tura jami’an fadakar da manoma sama da 1,800 a fadin kasar domin taimaka wa manoma da ilimin zamani kan hanyoyin noma.

Kara karanta wannan
An jibge jami'an tsaro, sun hana mutane zirga zirga a kananan hukumomi 2 a jihar Kano
A cewarsa, jami’an za su taimaka wajen bai wa manoma shawarwari kan inganta amfanin gona da amfani da dabarun zamani.
NADF ta tallafa wa manoma
Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa NADF ta riga ta tallafa wa manoman citta sama da 5,000 da matsalar cututtuka ta shafa a jihar Kaduna.
Haka kuma, ya ce hukumar ta taimaka wa manoman albasa da ambaliyar ruwa ta shafa a jihohin Kebbi da Sokoto.
Ya ce irin wadannan matakai na daga cikin kokarin gwamnati wajen kare harkar noma daga matsalolin da ke kawo cikas ga samar da abinci.

Source: Twitter
Martanin gwamnan jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya bai wa bangaren noma muhimmanci, a cewar rahoton PM News.
Ya bayyana shirin rabon takin a matsayin wani muhimmin mataki wajen kara yawan amfanin gona da tabbatar da samar da abinci.
A nasa bangaren, Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya ce shirin na nuna kudirin gwamnatin tarayya na tallafa wa kananan manoma da kuma bunkasa samar da taki a cikin gida.
Shettima ya ƙaddamar da shirin rabon taki
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da rabon buhunan taki 515,720 na urea da NPK ga manoma 128,930 a jihohi 25 da birnin tarayya Abuja.
Wannan yana daga cikin wani yunƙuri na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙarfafa harkar noma da bunƙasa samar da abinci a ƙasar nan.
Mataimakin shugaban kasar ya ƙaddamar da shirin ne a Abuja a ƙarƙashin shirin tallafin kayan noma na Renewed Hope - FISP, wanda Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa (NADF) ke gudanarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
