Sojoji Sun Dira Maboyar 'Yan Ta'adda a Katsina, an Kashe Tantirai da Kwato Manyan Makamai

Sojoji Sun Dira Maboyar 'Yan Ta'adda a Katsina, an Kashe Tantirai da Kwato Manyan Makamai

  • Dakarun sojojin Najeriya sun ci gaba da hana 'yan ta'adda sakat a jihar Katsina ta hanyar mai samame a maboyarsu cikin daji
  • Sojojin sun sake kai wani harin bazata a maboyar 'yan ta'adda da ke karamar hukumar Matazu inda suka yi musayar wuta da hatsabibai
  • A yayin artabun, sojojin sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda tare da raunata wasu daga cikinsu da kuma kwato makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Rundunar sojoji ta Brigade 17 da ke gudanar da aikin "Operation Clean Sweep III" ta kashe mutane biyu da ake zargi 'yan ta'adda ne a jihar Katsina.

Rundunar sojojin ta ƙwato manyan makamai da sauran kayayyaki a lokacin wani farmakin ba-zata na da aka kai a maboyar 'yan ta'adda da ke karamar hukumar Matazu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige 'yan bindiga tare da kama wasu a Kaduna

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Katsina
Dakarun sojojin Najeriya a maboyar 'yan ta'adda a Katsina Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda

Majiyoyin sojoji sun bayyana cewa an gudanar da aikin ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Yunin 2026 a ƙauyen Ginchawa, biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu kan ayyukan 'yan ta'adda a yankin.

Dakarun sojojin sun far wa maboyar hatsabiban ne cikin ba-zata, lamarin da ya sa 'yan ta'addan suka gigice.

'Yan ta'addan sun yi ƙoƙarin nuna tirjiya ga farmakin, amma dakarun sojojin sun murƙushe su da gagarumin ƙarfin wuta, wanda hakan ya tilasta musu guduwa zuwa cikin dazukan da ke kewaye da su.

A cewar majiyoyin, nan take sojojin suka bi sahun 'yan ta'addan da ke tserewa ta hanyoyin da suka gudu, har sai da aka rasa sahunsu daga ƙarshe.

Sojoji sun kwato makamai

Binciken da aka gudanar a maboyar bayan hakan ya kai ga ƙwato manyan bindigogi na PKT guda biyu, bindigar gargajiya guda ɗaya, rumbun harsasai na AK-47 guda ɗaya, da kuma harsasai kirar NATO masu kaurin 7.62mm guda 75.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun hallaka hatsabibin jagoran 'yan bindiga a Kebbi

Sauran kayayyakin da aka ƙwato a lokacin aikin sun haɗa da babura guda uku, wayoyin salula guda biyu, na'urar sadarwa ta Motorola guda ɗaya, kayan sojoji guda ɗaya, shanu biyu, da kuma awaki huɗu.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Majiyoyin sun bayyana cewa babu wani soja da ya rasa ransa ko ya ji rauni a lokacin gudanar da aikin.

Sun ƙara da cewa an kashe 'yan ta'adda biyu, yayin da ake zaton cewa wasu da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga, ganin cewa an gano alamun jini a cikin maboyar da kuma hanyoyin da ake zargin sun bi domin tserewa.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na Najeriya karkashin Operation Fansan Yamma (OPFY) sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin 'yan bindiga ne a jihar Kaduna.

Sojojin sun kuma cafke wasu 'yan bindiga huɗu tare da ƙwato dabbobin da aka sace a jerin hare-haren hadin gwiwa da suka gudanar.

Ayyukan da sojojin suka gudanar sun kai ga ƙwato makamai, harsasai, babura da na'urorin lantarki daga hannun wadanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng