Siyasar Najeriya
Jigon APC kuma mai neman takarar shugaban kasa, Alhaji Bayero Lawal, ya maka jam’iyyar a kotu bisa zargin hana shi sayen fom din takara a zabe mai zuwa.
Jam'iyyar ADC ta ce Shugaba Bola Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 ba, tana mai zargin ya gabatar da takardun bogi ga INEC.
Jam'iyyar APM reshen jihar Legas ta bayyana cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya kamata 'yan adawa su tsaida a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce babu laifi idan malaman addini sun shiga siyasa, yana mai cewa malamin da ya shiga siyasa ya fi wanda ke yi wa 'yan siyasa addu'a kawai.
A labarin nan, za a ji cewa wata kungiyar Kiristoci ta kai karar tikitin Muslim Muslim da gwamantin Bola Tinubu ta dawo da shi wajen neman takarar shugaban kasa.
INEC ta wallafa takardun Bola Tinubu na takarar shugaban kasa a 2027, amma rashin bayanan firamare da sakandare ya sake tayar da muhawara daga ADC, Atiku da lauyoyi.
G100 ta bukaci yan adawa su hada kai su tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya a zaben 2027, tana mai cewa rabuwar kawunansu na barazana ga dimokuradiyya.
PDP ta bayyana cewa tana jiran hukuncin kotu kan rikicin takarar gwamnan Gombe da ya shafi Farfesa Isa Pantami, tana mai cewa babu wani rikicin takara a jihohi.
A labarin nan, za a ji abin da ya jawo rikici a tafiyar OK movement duk da Peter Obi ya roki magoya bayansa da su bar wannan magana a cikin gida, kar ta fita waje.
Siyasar Najeriya
Samu kari