Gobara Ta Tashi a Ukraine bayan Rasha Ta Harba Daruruwan Jiragen Yaki

Gobara Ta Tashi a Ukraine bayan Rasha Ta Harba Daruruwan Jiragen Yaki

  • Jami’an Ukraine sun ce jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami na Rasha sun kai wani babban hari kan Kyiv a daren Lahadi
  • An ce sun kashe mutane da dama a babban birnin tare da haddasa gobara a wani tsohon coci mai tarihi da ke cikin wuraren tarihi
  • Magajin garin birnin Kyiv, Vitali Klitschko ya bayyana cewa mutum 28 ne suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai cikin dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ukraine - Hare-haren Rasha sun kashe mutum tara tare da janyo gobara a wani babban coci a Kyiv, kamar yadda jami’an kasar suka bayyana.

Mutum huɗu sun mutu a hare-haren da aka kai wa babban birnin Ukraine, yayin da ma’aikatan agaji biyar suka mutu yayin ƙoƙarin kashe gobarar da wani hari ya haddasa a birnin Kharkiv da ke Arewa maso Gabashin ƙasar.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 1 da harin Yelewata, Lakurawa sun kashe fiye da mutane 15 a Kebbi

Wani waje da aka kai hari Ukraine
Yadda Rasha ta harba makamai wasu wurare a Ukraine. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Harin Rasha ya ruguza coci

BBC ta wallafa cewa an yi mummunar barna a Cocin Dormition mai tarihi daga ƙarni na 11, abin da Shugaba Volodymyr Zelensky ya kira:

“Daya daga cikin manyan laifuffukan Rasha kan al’adun Kiristanci a yau”.

Sai dai duk da maganar da shugaba Volodymyr Zelensky ya yi, kasar Rasha ta musanta kai hari kan wurin.

A lokaci guda kuma, wani hari da jirgin maras matuƙi na Ukraine ya kai a birnin Tula na Rasha ya kashe mutum uku tare da jikkata wasu uku, ciki har da jariri mai shekara ɗaya, kamar yadda jami’an yankin suka ce.

Harin ya jawo gobara a Ukraine

Hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami sun haddasa gobara a gine-gine da motoci, tare da katse wutar lantarki ga fiye da mutum 140,000 a Kyiv, kamar yadda magajin garin birnin, Vitali Klitschko, ya bayyana.

Rahotanni sun nuna cewa yawancin sassan Ukraine na ƙarƙashin gargaɗin hare-haren sama a safiyar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Iran da Amurka sun cimma yarjejeniya, farashin mai ya fara sauka kasa

Hare-haren da aka kai wa Kyiv, waɗanda suka shafi gidajen zama da dama, sun jikkata aƙalla mutum 23, yayin da wasu mutum biyar suka jikkata a Kharkiv.

Volodymyr Zelensky da Vladimir Putin
Volodymyr Zelensky a hagu da Vladimir Putin a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Makaman da Rasha ta harba

Zelensky ya ce Rasha ta harba jimillar makamai masu linzami 70 da jirage marasa matuƙa 611 a harin da aka kai cikin dare, yana mai cewa daga baya an kashe gobarar.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya taya shugaban Ukraine Allah-wadai da harin da kasar ta ce Rasha ta kai mata.

“Babu wani dalili da zai iya tabbatar da wannan hari kan abubuwan tarihi na duniya,”

In ji Macron a shafin X.

Hare-haren sun zo ne gabanin taron shugabannin ƙasashen G7 da za a gudanar a wannan makon a France, inda za a tattauna batun yaƙin Ukraine.

Yakin Iran: Rasha ta magantu

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Rasha ta yi magana kan yakin da Iran ta yi da Amurka kafin cimma yarjejeniya.

A lokacin da aka fara kai sababbin hare-hare, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar da cewa komawa teburin sulhu ne ya fi dacewa.

A daidai lokacin da abubuwa suka nemi su dagule a Gabas ta Tsakiya, gwamnatin Rasha ta bukaci kasashen su kai zuciya nesa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng