Yaron Janar Rabe Ya Nemi Amsa kan Yadda Gwamnati Ta 'Ceto' Gawar Mahaifinsu

Yaron Janar Rabe Ya Nemi Amsa kan Yadda Gwamnati Ta 'Ceto' Gawar Mahaifinsu

  • Iyalan marigayi Janar Rabe Abubakar sun nemi bayani kan yadda aka karɓo gawarsa daga hannun ’yan bindigan da suka yi garkuwa da su
  • Yaronsa, Isiyaka Rabe Abubakar, ya ce har yanzu mahaifiyarsa na tsare a hannun masu garkuwa da mutane duk da an iya karɓo gawar mahaifinsu
  • Ya bayyana halin alhini da takaici da suka shiga daga lokacin da aka sace mahaifinsu zuwa lokacin da aka karbo gawarsa bayan ya rasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Iyalan marigayi Manjo Janar mai ritaya, Rabe Abubakar, sun buƙaci gwamnatin jihar Katsina ta yi bayani kan yadda aka samu aka dawo da gawar tsohon jami’in sojan daga hannun ’yan bindiga.

Sun nemi bahasi ne ganin cewa har yanzu matar tsohon sojan da aka sace su tare na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutanen.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani da Janar Rabe Abubakar ya mutu a hannun 'yan bindiga

Iyalan Janar Rabe Abubakar mai ritaya na son sanin yadda aka karɓo gawar mahaifinsu
H-D: Yadda aka gudanar da jana'izar Manjo Janar Rabe Abubakar ritaya, tsohon babban jami'in lokacin yana da rai Hoto: MB Marafa/HQ Nigerian Army
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da DW Hausa, ɗan marigayin, Isiyaka Rabe Abubakar, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa mahaifiyarsa ta samu ’yanci, yana mai cewa har yanzu tana tsare a hannun masu garkuwa da ita.

Yadda aka sace Janar Rabe a Katsina

Nigerian Tribune ta wallafa cewa an yi garkuwa da Janar Rabe Abubakar da matarsa, Amina, a ranar 30 ga Mayu, 2026, yayin da suke tafiya a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindiga sun tare su ne a kusa da ƙauyen Zakin Baure da ke ƙaramar hukumar Matazu, inda direbansu ya samu raunukan harbin bindiga.

Mutuwar tsohon Janar din ta jawo ce-ce-ku-ce, musamman game da musabbabin rasuwarsa da kuma yadda aka samu aka dawo da gawarsa.

Iyalan Janar Rabe sun shiga tashin hankali

Da yake magana kan yadda aka karɓo gawar mahaifinsa, Isiyaka ya ce iyalansu ba su da amsar wannan tambaya, yana mai cewa ya kamata a nemi bayani daga gwamnati.

Kara karanta wannan

Yadda aka birne Janar Rabe da ya rasu a hannun 'yan bindiga cikin jimami a Katsina

Ya ce:

“Mutane da dama sun ga sanarwar cewa za a yi jana’iza da ƙarfe shida. Sai suka tambaye ni yadda aka dawo da gawar. Na ce ba ni da amsar wannan tambayar. Gwamnati ce ya kamata a tambaya. Ni ma ina son sanin yadda aka kawo gawar.”
Iyalan Janar Rabe sun ce ba su san yadda aka karɓo gawar mahaifinsu ba
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Matashin ya ce iyalansu sun karɓi rasuwar mahaifinsa a matsayin ƙaddarar Allah, tare da fatan Allah Zai saka masa da alheri.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tawali’u, riko da addini da son zaman lafiya, wanda bai cutar da kowa ba a rayuwarsa.

Isiyaka ya karkare da rokon gwamnan jihar Katsina, yana mai cewa har yanzu iyalansu na jiran dawowar mahaifiyarsa daga hannun masu garkuwa da mutane.

Janar Rabe ya rasu a hannun ƴan bindiga

A baya, mun kawo labarin cewa Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Manjo Janar na rundunar sojojin Najeriya, Rabe Abubakar (mai ritaya).

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi maganar mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan Bindiga

Ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini da gwamnati ta bayyana cewa yana fama da su.

Gwamna Dikko Radda na Katsina ya lamarin a matsayin babban rashi ga jihar da ma Najeriya baki daya, tare da mika ta'aziyya ga iyalan marigayi Manjo Janar Rabe mai ritaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng