Kwamacala a APC: An Samu 'Yan Takarar Gwamna 2 bayan Zaben Fitar da Gwani

Kwamacala a APC: An Samu 'Yan Takarar Gwamna 2 bayan Zaben Fitar da Gwani

  • Rikici ya barke a APC reshen Abia bayan fitowar ‘yan takara biyu daga zaben fidda gwani na gwamna gabanin na shekarar 2027
  • Mambobin kwamitin gudanarwar APC 13 sun amince da Henry Ikoh a matsayin dan takarar bai daya bayan janyewar Mascot Uzor Kalu
  • Duk da matsayar SWC, an bayyana Eric Opah a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani bayan samun kuri’u 126,977

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia - An rikici a APC reshen Abia kan wanda zai zama dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2027 bayan bayyanar ‘yan takara biyu daga zaben fitar da gwani.

A ranar Alhamis, mambobi 13 cikin 18 na kwamitin gudanarwar APC a Abia sun gana a Umuahia tare da amincewa da Cif Henry Ikechukwu Ikoh.

Kara karanta wannan

APC ta jaddada yadda tsarin zaben fitar da gwani na shugaban kasa zai kasance

Rikici ya barke a APC kan samu yan takarar gwamna 2
Taswirar jihar Abia da aka samu matsala a yayin fitar da dan takarar gwamna. Hoto: Legit.
Source: Original

An bayyana cewa shawarar ta biyo bayan tattaunawar sirri da shugabannin jam’iyya da mafi yawan mambobin kwamitin gudanarwar APC suka yi na dogon lokaci, cewar Punch.

Abia: An zabi dan takarar gwamnan APC

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya ce sun amince da Ikoh ne saboda kwarewarsa, shugabanci nagari da kuma damar hada kan jam’iyyar gaba daya.

Mambobin kwamitin sun bayyana cewa Abia na bukatar shugabanci mai hangen nesa a wannan lokaci, suna masu cewa Ikoh yana da cikakkun kwarewar jagoranci.

Sanarwar da suka fitar ta ce bayan tattaunawa mai zurfi, shugabannin APC a Abia sun amince da Henry Ikoh a matsayin dan takarar bai daya.

Sakataren tsare-tsare na APC a Abia, Hon. Emeka Okorafor, ya tabbatar wa manema labarai a Umuahia cewa sun amince da Ikoh ne bayan janyewar Mascot Kalu.

Ya ce janyewar Mascot Kalu daga takara ya bar Henry Ikoh a matsayin dan takarar gwamna daya tilo da APC ke da shi.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, APC ta tsayar da 'dan takarar gwamna a jihar Gombe

APC ta fitar da ƴan takarar gwamna 2 a Abia
Henry Ikoh da Eric Opah da ake tababa bayan tsayar da su a matsayin ƴan takarar gwamna a APC. Hoto: Henry Opah, Abia Reporters.
Source: Facebook

Daga cikin wadanda suka sanya hannu akwai sakataren jam’iyya Chidi Avaja, mataimakinsa Benedict Godson da mataimakin shugaban APC Chinedu Ihesinulo.

Sauran sun hada da shugaban matasa Jerry Awa, shugabar mata Erondu C.C, ma’aji John Ajuziogu da mai ba jam’iyya shawara kan shari’a, cewar The Sun.

An sake fitar da wani dan takara

Sai dai bayan awanni kadan da fitar da matsayar kwamitin, aka bayyana Chief Eric Opah a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani.

Shugaban kwamitin zaben gwamna na APC a Abia, Hon. Bartho Along, ya ce Opah ya samu kuri’u 126,977 yayin da Ikoh ya samu 5,905.

Along ya yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin lumana tare da nuna gamsuwa kan yadda mambobin jam’iyyar suka nuna da’a da kwanciyar hankali.

Ana ganin shugabancin jam'iyyar APC na kasa ne zai yanke hukuncin karshe kan wanda zai rike tikitin gwamna na jam’iyyar a Abia.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya samu shiga da APC ta zabi dan takararta na gwamnan Kano a 2027

Na kusa da Wike ya samu takarar gwamna

A baya, an ji cewa wani makusancin ministan Abuja, Nyesom Wike kuma dan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo bayan kasancewarsa shi kadai a zaɓen fitar da gwani da aka yi a ranar Alhamis.

Chinda ya yi alƙawarin gudanar da mulki cikin gaskiya, tsoron Allah da bin doka idan aka zaɓe shi bayan shan alwashi kan tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.