Sanata Barau Ya Yi Magana bayan Gwamna Abba Ya Samu Tikitin APC a Kano
- Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a babban zaben shekarar 2027 da za a gudanar a Kano
- Mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya taya Gwamna Abba Kabir murna kan wannan nasarar da ya samu
- Sanata Barau ya yi fatan cewa mutanen Kano za su sake yi wa Gwamna Abba ruwan kuri'u a zaben 2027 domin samun wa'adi na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya taya gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murna.
Sanata Barau ya taya Gwamna Abba murna ne biyo bayan tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC gabannin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata Barau ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026.
An tabbatar da Gwamna Abba ne ranar Alhamis, 21 ga watan Mayun 2026 a lokacin wani taro da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha Stadium.
Sanata Barau ya taya Gwamna Abba murna
A cewar Sanata Barau, tabbatarwar ta biyo bayan ƙa'idojin da ke ƙunshe cikin dokar zaɓe da kuma jagororin jam'iyyar APC.
Sanata Barau ya bayyana cewa shi ne ya tura buƙatar tabbatar da gwamnan, yayin da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya goyi bayan buƙatar.
Barau ya ce shugaban kwamitin zaben fitar da gwani na APC na daga hedkwatar jam'iyyar ta ƙasa, Mukhtar Shagari, daga baya ya ayyana Gwamna Abba a matsayin ɗan takarar gwamna na APC na zaɓen 2027 a jihar Kano.
“Ina taya Mai girma gwamnan jama'a, Injiniya Abba Kabir Yusuf, murna ta gaske kan zamansa a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar mu na babban zaɓen 2027."
- Sanata Barau Jibrin
Barau yana fatan mutanen Kano su zabi Abba
Ya nuna kyakkyawan fatan cewa mazauna jihar Kano za su sabunta wa’adin mulkin Gwamna Abba a lokacin zaɓen gwamna da aka tsara gudanarwa ranar 6 ga watan Fabrairu, 2027.
“Insha Allah, mutanen kirki na jihar Kano, waɗanda ke ci gaba da shaidawa da kuma yaba ayyukan ci gaba da dama a faɗin jihar, za su sake ba shi amana da kuri'unsu."
- Sanata Barau Jibrin

Source: Facebook
Fatan Barau kan Tinubu da 'yan takarar APC
Sanatan ya kuma nuna yakinin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ’yan takarar APC masu neman kujerun majalisa za su samu nasara a zaɓubbukan da za a gudanar ranar 16 ga watan Janairu, 2027.
“Tare, za mu ci gaba da yin aiki ba tare da gajiya ba domin tunkarar ƙalubalen da mutanenmu ke fuskanta tare da samar da ƙarin romon dimokuraɗiyya."
- Sanata Barau Jibrin
Gwamna Abba ya sulhunta Barau da Gwarzo
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sulhunta Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Tijjani Gwarzo.
Matakin sulhun da Gwamna Abba ya dauka, ya buɗe hanyar samun haɗin kai gabanin kakar zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.
Taron sulhun ya ƙare ne da sanarwar da Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bayar na janyewa daga takarar sanata domin marawa Sanata Barau Jibrin baya.
Asali: Legit.ng

