Kungiyar Musulmi Ta Goyi bayan Mafitar da Matawalle Ya Kawo kan Matsalar Tsaron Najeriya
- Kungiyar musulmi ta Nigerian Muslims Forum ta yabi Bello Matawalle kan kira da a nemi taimakon Allah wajen magance rashin tsaro
- Kungiyar ta ce yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane a Najeriya na bukatar haɗin gwiwar matakan tsaro da kuma addu’a
- Ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya shirya babban taron addu’a na kasa domin neman zaman lafiya yayin da kasar ke fuskantar tabarbarewar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Wata Kungiyar Musulmi 'Nigerian Muslims Forum' ta yaba wa Karamin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, kan kalaman da ya yi game da sha'anin tsaro a baya-bayan nan.
Kungiyar ta goyi bayan Matawalle kan shawarar da ya bayar ta neman a dage da addu’a da neman taimakon Allah wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

Kara karanta wannan
2027: Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya gana da jagororin tafiyar Obi da Kwankwaso

Source: Twitter
Sakataren kungiyar, Farfesa AbdulKadir Umar Na’amo, ne ya bayyana hakan a Gusau, jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Matawalle ya bukaci yan Najeriya su dage da addu'o'in neman zaman lafiya domin hakan zai taimaka wajen nasarar jami'an tsaro.
Musulmi sun fara goyon bayan Matawalle
Da take tsokaci kan haka, kungiyar ta ce duk da muhimmancin ayyukan soji da sauran dakaru, wajibi ne ’yan Najeriya su ci gaba da neman taimakon Ubangiji domin kawo karshen matsalolin ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauransu.
Farfesa Na’amo ya ce matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta masu matukar sarkakiya, na bukatar a hada matakan zahiri da na addu'a.
A cewarsa, addu’a wata babbar hanya ce da za ta iya taimakawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.
Ya kara da cewa:
“Matsalolin tsaron Najeriya sun zarce abin da karfin makami kadai zai iya warwarewa. Addu’a da neman taimakon Allah suna da muhimmiyar rawa wajen samun mafita.”

Kara karanta wannan
Matawalle ya tsage gaskiya, ya ce Allah kadai zai iya magance matsalar tsaron Najeriya
An yaba wa Tinubu kan batun tsaro
Kungiyar ta kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kokarin da yake yi na magance matsalar rashin tsaro.
Ta ce an samu ci gaba a wasu yankuna musamman a Arewa maso Yamma idan aka kwatanta da halin da gwamnati ta gada.
A cewar kungiyar, gwamnatin Tinubu ta kara karfafa ayyukan soji, tattara bayanan sirri da kuma tallafawa hukumomin tsaro domin yaki da miyagun laifuka.

Source: Facebook
An nemi shirya taron addu’ar kasa
Kungiyar ta bukaci shugaban kasa ya kira wani babban taron addu’o'i na kasa wanda zai hada malaman addinin Musulunci da Kirista, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki daga dukkan shiyyoyin Najeriya.
Ta ce irin wannan taro zai hada kan ’yan Najeriya wajen neman jagoranci, kariya da taimakon Allah a yakin da ake yi da masu tada kayar baya.
Matawalle ya kawo mafita ga Najeriya
An ji cewa Karamin Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, ya ce Allah ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.

Kara karanta wannan
'Tinubu ya dawo da zaman lafiya a wasu yankuna': Matawalle ya hango nasara a 2027
Ya ce matsalar tsaro ta shafi kowa da kowa ba tare da la'akari da jam'iyya ko addini ba, don haka ya kamata 'yan Najeriya su haɗa kai da jami'an tsaro domin kawo ƙarshenta.
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan Najeriya da ke farin ciki da abin da ke faruwa, amma wasu daga cikin 'yan adawa suna amfani da matsalar domin nuna gazawar gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng