Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Borno, an Kashe Tantirai kusan 30

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Borno, an Kashe Tantirai kusan 30

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai hare-hare ta sama kan maboyar 'yan ta'adda a jihar Borno, inda suka hallaka da dama daga cikinsu
  • Sojojin sun kai hare-haren ne wadanda suka yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda a maboyarsu da ke yankin Tumbuns na jihar Borno
  • Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar ceto wasu mutane da suka hada da maza da mata wadanda 'yan ta'adda suka yi yunkurin sacewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Sashen dakarun sama na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ya kashe mambobin 'yan ta'adda da ba su gaza 27 ba a jihar Borno.

Sojojin sun samu nasarar ne a hare-haren sama da suka kai a maboyar 'yan ta'adda a yankin Tumbuns na jihar Borno.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Olufemi Oluyede Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta sanya a shafinta na X a ranar Lahadi, 14 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Neja, an kashe mutane da kona gidaje

Yadda sojoji suka kashe 'yan ta'adda

Rundunar sojojin ta ce an kashe 'yan ta'adda 12 a wani harin sama da aka kai a Dawoshe da ke karamar hukumar Kukawa.

Hakazalika ta ce an kashe wasu 'yan ta'adda 15 a wani harin na daban da aka ƙaddamar a Metele da ke karamar hukumar Guzamala.

Rundunar sojojin ta ce hare-haren na cikin jerin ayyukan da aka gudanar a faɗin ƙasar a cikin ƙarshen makon da ya gabata.

Sojoji sun gudanar da ayyukan tsaro

A cewarta, ayyukan da aka gudanar sun yi sanadiyyar kama mutane 10 da ake zargi da aikata laifuka, ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su, da kuma ƙwato makamai, harsashi, motocin da aka sace da sauran abubuwa.

Ayyukan da aka gudanar bisa bayanan sirri sun haɗa da haɗin gwiwar dakarun ƙasa da na sama, kuma an gudanar da su ne a jihohin Borno, Plateau, Nasarawa da Akwa Ibom, da Babban babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun jefa bama bamai a maboyar 'yan ta'adda a Borno, an kashe kwamandoji

An kwato kayayyaki a hannun 'yan ta'adda

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Dakarun sojojin ƙasa a Borno sun kuma kama wani da ake zargi da ta'addanci a kan hanyar Mandara Girau Sabon Gari a Ƙaramar Hukumar Biu."
"Kayan da aka ƙwato sun haɗa da tarin kayan abinci da ake kyautata zaton na 'yan ta'adda ne, kamar su kayan abinci, na'urorin sadarwa, bargo, magungunan kashe ciyawa da batura."
“Haka kuma, a wani lamari na daban kusa da Kareto, dakarun sun dakile yunƙurin yin garkuwa da mutane sannan suka yi nasarar ceto fararen hula shida da suka haɗa da maza uku da mata uku ba tare da sun samu rauni ba."
Sojoji sun ceto mutane daga hannun 'yan ta'adda
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan ISWAP a wasu hare-hare a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun lalata motoci da dama a lokacin wasu hare-haren sama da aka kai a kewayen Cross Kauwa da Ali Sherifti da ke Arewacin jihar Borno.

Hare-haren da dakarun sojojin suka kai sun yi nasarar kashe aƙalla mutane tara da ake zargi 'yan ta'addan ƙungiyar ISWAP

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng