Jirgin Sama Dauke da Sojoji Ya Yi Mummunan Hatsari, Dakaru 5 Sun Bakunci Lahira a India
- Rundunar sojojin saman India ta tabbatar da rasa wasu daga cikin dakarunta sakamakom hatsarin da ya ritsa da jirgin da suke ciki
- Jirgin saman wanda ake sufuri tare da daukar kayayyaki da shi ya gamu da hatsari ne a jihar Assam wanda ke a yankin Arewa maso Gabashin kasar
- Rundunar sojojin saman ta bayyana cewa jami'anta guda biyar ne suka mutu, inda ta ba da tabbacin cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Birnin New Delhi, India - Wasu jmi’an rundunar sojojim saman India sun gamu da hatsarin jirgin sama wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsu.
Jam'ian rundunar sojojin saman India su biyar ne suka riga mu gidan gaskiya bayan da jirgin da suke tafiya a cikinsa ya yi hatsari a jihar Assam da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa jami'ai ne suka tabbatar da hatsarin jirgin a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.
Jirgin sama ya yi hatsari a India
Jirgin saman na sufuri nau'in Antonov An-32 ya “samu hatsari” ne yayin wani “aikin yau da kullun” a yankin Jorhat na jihar Assam, kamar yadda rundunar sojan saman India ta bayyana a cikin wata sanarwa ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Ana nan ana gudanar da aikin kula da inda hatsarin ya faru da kuma binciken farko a halin yanzu."
Hakazalika rundunar sojojin saman ta ƙara da cewa an ƙaddamar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Rundunar sojan saman India tana amfani da rukunin jiragen sama na An-32 kusan 105 domin jigilar mutane da kayayyaki.
Babban hatsari na ƙarshe da ya shafi jirgin mai injina biyu ya auku ne a shekarar 2019 a jihar Arunachal Pradesh, kusa da iyaka da ƙasar China, inda mutane 13 suka mutu.

Source: Twitter
Rundunar sojojin sama ta yi ta'aziyya
A wata sanarwa ta daban a shafinta na X, rundunar sojojin saman India ta mika sakon ta'aziyyarta kan rasuwar jami'an.
Sanarwar na cewa:
"Rundunar sojojin saman India tana bayyana matsanancin alhini kan rashin jami’ai biyar a hatsarin jirgin An-32 a Jorhat, Assam."
"Sqn Ldr Prashant Singh, Flt Lt Shubham Kumar, Sgt Jitendra Sharma, Agniveervayu Khemaram Kumawat da Agniveervayu Danish Alam sun sadaukar da rayuwarsu a lokacin gudanar da aiki."
"Hukumar IAF tana mika ta'aziyya ga iyalan mamatan kuma tana tsaye daram tare da su a wannan lokaci na baƙin ciki."
Jirgin sama ya yi hatsari a Pakistan
A wani labarin kuma, kun ji cewa jirgin sama na helikofta na rundunar sojojin Pakistan ya faɗi kusa da birnin Muzaffarabad da ke yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi.
Dakarun sojojin ƙasar sun bayyana cewa Jirgin ya gamu da hatsari ne sakamakon matsalar inji, inda suka ƙara da cewa babu wanda ya tsira da ransa.
Sai dai, sanarwar da dakarun sojojin suka fitar ba ta bayyana takamaiman adadin mutanen da suka mutu ba, sakamakon hatsarin da jirgin ya yi.
Asali: Legit.ng

