Bidiyo: Yadda Jami'an ICPC Suka Hana Jagororin Jam'iyyar ADC Ganawa da El Rufai
- Jam’iyyar ADC ta zargi ICPC da hana shugabanninta ganawa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a hedikwatar hukumar Abuja
- ADC ta ce yadda aka jibge jami’an tsaro a wajen hedikwatar hukumar ICPC ya nuna ana amfani da hukumomi wajen tsoratar da ‘yan adawa
- Jam’iyyar hadakar 'yan adawar ta bukaci a bai wa El-Rufai damar ganin iyalansa, likitoci da lauyoyinsa cikin gaggawa ba tare da takura ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar ICPC da hana shugabannin jam’iyyar damar ganin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, wanda ke tsare a hannunta.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa mai zafi da ta fitar ranar Juma’a bayan wata tawaga ta shugabanninta ta kasa samun damar ganawa da El-Rufai a hedikwatar ICPC da ke Abuja.

Source: Twitter
Aregbesola da shugabanni sun je ICPC
Mai magana da yawun jam'iyyar Bolaji Abdullahi ne ya fitar da wannan sanarwa a shafinsa na X da misalin karfe 5:33 na yammacin yau.
Tawagar da ta kai ziyara ga El-Rufai ta kunshi sakataren jam’iyyar na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola; sakataren yada labarai, Bolaji Abdullahi; da sakataren kwamitin manufofi da kundin tsari, Salihu Lukman.
ADC ta ce tun kafin zuwan tawagar, ta rubuta wa shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu wasikar neman izinin ziyartar El-Rufai saboda damuwar da iyalansa suka nuna kan lafiyarsa da kuma zargin hana shi ganin likita da samun abinci.
A cewar ADC, yayin da shugabanninta ke jiran amsa daga hukumar, sai aka ga manyan motoci dauke da jami’an ‘yan sanda masu yawa sun mamaye harabar ICPC.
ICPC ta zargi hukumomin gwamnati
Sanarwar Bolaji ta ce hakan ya haifar da yanayi na tsoro duk da cewa shugabannin da suka je ba su dauke da makami kuma ba su yi wata barazana ba.
“Abin takaici ne yadda aka dauki ziyarar shugabannin jam’iyya zuwa ga wanda ake tsare da shi tamkar wata tarzoma da ta tunkari hukumar,” in ji
Jam’iyyar ta yi zargin cewa ana amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa lamba da tsoratar da 'yan adawa.
Ta ce yadda aka hana shugabanninta ganin El-Rufai ya kara jefa shakku kan yadda ake tafiyar da shari’ar da ake yi masa.
“Abin da muke gani yanzu yana kama da hukunta mutum ta hanyar tsare shi da ware shi domin karya masa gwiwa,” in ji sanarwar Bolaji.

Source: Twitter
Iyalan El-Rufai sun yi korafi
Jam’iyyar ta tuna cewa kwanakin baya matar El-Rufai, Hajiya Asia El-Rufai, ta yi zargin cewa an hana mijinta ganin likita tare da hana ta kai masa abinci lokacin da ta je ICPC da yamma.
ADC ta ce iyalan tsohon gwamnan sun kuma nuna damuwa cewa ana kawo cikas ga umarnin kotu da ya ba shi damar samun kulawar lafiya.
Da wannan, jam’iyyar ta bukaci ICPC ta bai wa iyalai, likitoci, lauyoyi da shugabannin jam’iyyar damar ganin El-Rufai ba tare da wani takura ba.

Kara karanta wannan
Baki ya yanka wuya, kotu ta ingiza keyar kakakin PDP zuwa kurkuku kan taba gwamna
Kalli bidiyon yadda aka hana shugabannin ADC shiga ganin El-Rufai a kasa, wanda Sopriala Membere ya wallafa a shafinsa na X:
Iyalan El-Rufai sun caccaki ICPC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Iyalan Malam Nasir El-Rufai, sun karyata zargin gano na’urar sauraren waya a gidan mahaifinsu da ke Abuja.
'Dan sa kuma dan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, ya ce zargin da hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta yi karya ne.
Iyalan sun ce binciken da aka yi a gidan haramtacce ne saboda takardar izinin bincike da ake zargin an yi magudi da ita.
Asali: Legit.ng

