Duk da Cika Bakin Amurka kan Sulhu, Iran Ta Ja Mata Layi, Ta Gindaya Sharuɗa
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi ƙarin haske kan batun tattaunawa da Amurka da ake magana a yau Lahadi 14 ga watan Yunin 2026
- Duk da ikirarin Donald Trump cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu, Tehran ta ce har yanzu ba ta yanke hukunci na karshe ba
- Har yanzu ana takun saka kan makomar shirin nukiliyar Iran da mashigin Hormuz, yayin da hare-haren Lebanon suka sake tayar da rikici
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa babu wata fa'ida a ci gaba da tattaunawa da Amurka.
Ta zargi Washington da kasa cika alkawuran da ta dauka yayin da ake ci gaba da yaki da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.

Source: Facebook
Sai dai babban mai shiga tsakani na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana a X cewa Amurka ba ta nuna niyyar cika alkawuranta ba.

Kara karanta wannan
Abin da muka sani kan yarjejeniyar da Amurka da Iran za su iya kullawa don kawo karshen yaki
Ya bayyana cewa idan Amurka ba ta da niyya ko karfin cika alkawari, babu amfanin ci gaba da wannan hanya.
Matsalar da ta taso game da harin Isra'ila
Sabuwar matsalar ta taso ne bayan Isra'ila ta sanar da kai hare-hare kan wuraren Hezbollah a kudancin Beirut, cewar Reuters.
Shugaban Amurka Donald Trump ya taba bayyana cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya tun ranar Lahadi mai zuwa.
Ya kuma ce nan take za a bude mashigin Hormuz domin zirga-zirgar jiragen ruwa bayan sanya hannu kan yarjejeniyar da ake tattaunawa.
Sharudan da Iran ta gindaya kan sulhu
Iran ta dage cewa duk wata yarjejeniya dole ta kunshi rikicin Lebanon, domin Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a kasar.
Brigediya Janar Mohammad Jafar Asadi ya gargadi Isra'ila cewa sabon harin da ta kai ba zai wuce ba tare da martani ba.
Wani jami'in Amurka ya ce yarjejeniyar da ake tattaunawa ta hada da batun Lebanon, bayan Hezbollah ta shiga yakin tun watan Maris.

Kara karanta wannan
Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran

Source: Getty Images
Tawagar Qatar ta isa Tehran
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya ce ba za a sanya hannu ranar Lahadi 14 ga watan Yunin 2026 ba.
Duk da haka, ya ce ba za a iya kawar da yiwuwar cimma yarjejeniyar cikin kwanaki masu zuwa ba.
Wata tawaga daga Qatar ta isa Tehran domin taimakawa wajen kammala tattaunawar da kuma ganin an cimma yarjejeniyar.
Bangarorin da ke rikici sun ci gaba da bayar da bayanai masu karo da juna kan abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa.
Iran ta nace cewa za ta ci gaba da rike ikon kula da mashigar Hormuz duk da matsin lambar Amurka.
Yakin Iran, Isra'ila ya illata Najeriya
Mun ba ku labarin cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana manyan abubuwan da suke kawo cikas a yaki da ta'addanci.
Musa ya daura alhakin kan yaƙe-yaƙen Isra'ila da Iran da na Rasha da Ukraine wanda suka matsaloli ga kasar.
Ya buƙaci Najeriya ta fara ƙera kayan tsaro a cikin gida, tare da samar da cikakken bayanan 'yan ƙasa domin taimaka wa hukumomis.
Asali: Legit.ng