Gwamna Radda Ya Yi Hassshe da Ya Ga Yawan Mutanen da Suka Fito Zaben Tinubu
- Gwamna Dikko Radda ya nuna kwarin gwiwarsa bayan ganin dubban jama'a sun fito zaben fitar 'dan takarar shugaban kasa na APC a Katsina
- A yau Asabar, 23 ga watan Mayu, 2026, APC ta shirya zaben kato bayan kato don tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin 'dan takara
- Duk da akwai wanda ke neman tikitin APC, Gwamna Radda ya ce yana da yakinin Tinubu ne zai lashe har babban zaben shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Tinubu da ‘yan takarar jam’iyyar APC za su yi nasara a babban zaɓen 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Asabar bayan kaɗa ƙuri’arsa a garin Radda da ke ƙaramar hukumar Charanchi, yayin zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa na APC wanda ke gudana yau Asabar.

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Gwamna Dikko Radda ya gamsu da fitowar jama'a
Gwamnan ya nuna gamsuwa da yadda dubban jama'a suka fito da kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a, yana mai cewa hakan ya nuna ƙarfin dimokuraɗiyya da kuma yadda ‘yan Najeriya ke ƙara amincewa da gwamnatin APC.
“Yau ita ce rana ta ƙarshe ta zaɓen fitar da gwani na APC inda mambobin jam’iyya ke tabbatar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar mu a zaɓen 2027.
“APC jam’iyya ce da ke bai wa mambobinta dama iri ɗaya da haƙƙin dimokuraɗiyya wajen zaɓen shugabanninsu. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi kaɗai ne ɗan takara ba; Stanley Osifo ma ya sayi fom ɗin takara kuma ya shiga zabe ”
Dikko Radda ya hango nasarar Tinubu
Radda ya ce ya haɗu da dubban magoya bayan APC a mazaɓarsa domin cika haƙƙinsa na ɗan ƙasa tare da nuna goyon baya ga neman wa’adi na biyu na Tinubu.

Kara karanta wannan
Bayan kai ruwa rana, jam'iyyar APC ta tsaida 'dan takarar gwamnan Yobe a zaben 2027
“Abin da muka gani yau ya ƙara mana ƙwarin gwiwa cewa da yardar Allah, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu wa’adi na biyu domin ci gaba da jagorantar harkokin ƙasa,” in ji gwamnan.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa al’ummar Katsina na ci gaba da biyayya ga APC tare da cikakken goyon baya ga shugabancin Tinubu, yana mai watsi da sukar da ake yi wa jam’iyya mai mulki.
“Duk hayaniyar da ake yi da ƙoƙarin ɓata mana suna ba gaskiya ba ne. Goyon bayan da ake bai wa Shugaba Tinubu a bayyane yake, kowa na iya ganin yadda mutane suka fito,” in ji shi.
Gwamnan Katsina ya samu tikitin APC
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta tabbatar da Dikko Umaru Radda a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Katsina a babban zaben 2027.
Wakilan jam’iyyar APC ne suka tabbatar da Gwamna Dikko Radda a matsayin dan takarar gwamna a zaben 2027 ta hanyar maslaha a ranar Alhamis da ta gabata.
A jawabin karɓar takara, Gwamna Radda ya gode wa wakilai, shugabannin jam’iyya da magoya baya bisa amincewar da suka nuna masa.
Asali: Legit.ng