Tuggar Ya Rasa Tikiti da Aka Sanar da Dan Takarar Gwamna na APC a Bauchi
- Jam'iyyar APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fitar da gwani domin zabar dan takarar gwamna da ta gudanar a jihar Bauchi
- Tsohon Ministan harkokin waje, Ambassada Yusuf Tuggar, wanda ya yi murabus domin yin takara, ya sha kaye a zaben fitar da gwanin
- Hakazalika, tsohon babban jami'i a kamfanin mai na kasa (NNPCL), Bala Maijama'a A. Wunti, ya gaza samun tikitin jam'iyyar APC a Bauchi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Tsohon Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya rasa tikitin jam'iyyar APC don tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi.
Yusuf Tuggar da Bala Maijama’a A. Wunti, tsohon babban jami’i a kamfanin mai na kasa (NNPCL), sun rasa damarsu ta lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC na zaɓen 2027 a jihar Bauchi.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwani na gwamna da na Majalisar dokoki na APC na jihar Bauchi, AIG John Abang (mai ritaya) ya sanar da sakamakon a safiyar ranar Asabar, 23 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC
Yusuf Tuggar ya sha kaye a Bauchi
A cewar AIG John Abang, tsohon Gwamna Mohammed Abubakar ya doke sauran masu neman takarar guda shida domin lashe tikitin, jaridar TheCable ta kawo rahoton.
Ya sanar da sakamakon inda ya bayyana cewa Mohammed Abubakar, wanda ya yi nasara, ya sami ƙuri’u 57,517; Yusuf Tuggar ya samu ƙuri’u 26,001, yayin da Nura Manu Soro ya samu ƙuri’u 13,638.
Sauran masu neman takarar sun haɗa da Bala Maijama’a A. Wunti, wanda ya samu ƙuri’u 13,648, Kabir Baba Ma’aji da ƙuri’u 8,157, Baba Abubakar Suleiman wanda ya samu ƙuri’u 7,688, da kuma Yakubu Yakubu Abdullahi wanda ya samu ƙuri’u 7,181.
M.A Abubakar ya taba rasa zaben gwamna
Gwamna mai ci a yanzu na jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya taɓa doke Mohammed Abubakar a zaɓen shekarar 2019.
Bala Mohammed ya tsaya takara ne kuma ya lashe zaɓen a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, yayin da Mohammed Abubakar ya sha kaye a matsayinsa na gwamna mai ci a lokacin a ƙarƙashin APC.

Kara karanta wannan
Bayan kai ruwa rana, jam'iyyar APC ta tsaida 'dan takarar gwamnan Yobe a zaben 2027
Yusuf Tuggar yana cikin rukunin farko na waɗanda aka ba wa muƙamai waɗanda suka bi umarnin Shugaba Bola Tinubu na cewa duk masu neman muƙaman zaɓe a shekarar 2027 su yi murabus kafin ranar 31 ga watan Maris, 2027.

Source: Original
Wali ya zama dan takarar APC a Yobe
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta sanar da dan takararta na gwamna a jihar Yobe bayan kammala zaben fitar da gwani.
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe, Alhaji Baba Malam Wali, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.
An ayyana Malam Wali mai shekaru 68 a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamna da aka gudanar a fadin kananan hukumomin jihar Yobe.
Asali: Legit.ng