Ana Shirin Zaben 2027, Malamin Duba Ya Gargadi Atiku kan Sake Tsayawa Takara
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya samu gargadi kan sake tsayawa takara a 2027 da ake tunkara a Najeriya
- Malamin duba, Satguru Maharaj Ji wanda ya gargadi Atiku ka da ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 mai zuwa
- Maharaj Ji ya ce ya dace a bar yankin Kudu ya kammala wa’adin shekaru takwas kamar yadda Muhammadu Buhari daga Arewa ya yi mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wanda ya kafa kungiyar One Love Family, Satguru Maharaj Ji ya yi magana game da takarar Atiku Abubakar a zaben 2027.
Malamin ya gargadi tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan takarar zaben shekarar 2027 da ake tunkara a kasar.

Source: Facebook
An buƙaci Atiku Abubakar ya bar da takara
A cikin sanarwar da ya aikewa Tribune, Maharaj Ji ya ce bai kamata Atiku ko sauran ‘yan Arewa su tsaya takara ba a 2027.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi karin haske kan zargin shirin sauya sunan Najeriya, rusa shari'ar Musulunci
Ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar siyasa tsakanin Arewa da Kudu wadda ta tsara yadda ake musayar mulki domin tabbatar da daidaito a Najeriya.
Maharaj Ji ya ce dole ne yankin Kudu ya kammala shekaru takwas a Aso Rock kamar yadda yankin Arewa ya yi lokacin mulkin Muhammadu Buhari.
Shawarar da Maharaj ya ba dattawan Arewa
Ya kara da cewa dattawan Arewa da sauran masu fada a ji su shawo kan Atiku da sauran masu neman takara su hakura.
Ya ce:
“Dole ne a bar Kudu ta kammala wa’adinta na shekaru takwas a Aso Rock kamar yadda Arewa ta yi a gwamnatin Buhari da ta gabata.”

Source: Twitter
Matsalar da tsayawar Atiku takara za ta jawo
Jagoran addinin ya ce shirin sake tsayawar Atiku zai iya haddasa rikicin siyasa tare da kara dagula zaman lafiya kafin babban zaben 2027, cewar Daily Post.
Maharaj Ji ya zargi wasu manyan ‘yan Arewa da taimakawa wajen tabarbarewar matsalolin siyasa da tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta yanzu.
Ya soki ci gaba da burin Atiku na neman shugabanci duk da cewa ya dade yana cin moriyar mukaman gwamnati a rayuwarsa.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa
Gargadin da Maharaj ya yi kan takara a 2027
Maharaj Ji ya yi gargadi cewa duk wani mataki da zai kawo tangarda ga tsarin siyasar yanzu na iya haifar da tashin hankali mara amfani nan gaba.
Ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da biyayya ga kundin tsarin mulki domin kare hadin kai yayin shirye-shiryen babban zaben kasar wanda ake ganin zai yi zafi sosai.
An gargadi Jonathan kan takarar 2027
Mun ba ku labarin cewa an shawaci Goodluck Jonathan da kada ya nemi takarar kujerar shugaban ƙasa a 2027, duk da kiran da wasu magoya baya ke yi masa.
Primate Henry Chukwudum Ndukuba ne ya ba wa tsohon shugaban ƙasar wannan shawarar a wani taro da aka ɗauka a cikin wani bidiyo da ke yawo.
A cikin bidiyon, wanda ya fara haifar da martani daban-daban daga ’yan Najeriya, an hango tsohon shugaban ƙasar tare da wani tsohon shugaban Najeriya, Yakubu Gowon.
Asali: Legit.ng