Kotu Ta Ba Hukumar INEC Umarnin Soke Rajistar ADC da Wasu Jam'iyyun Siyasa 4

Kotu Ta Ba Hukumar INEC Umarnin Soke Rajistar ADC da Wasu Jam'iyyun Siyasa 4

  • Babbar kotun tarayya ta umarci hukumar INEC ta soke rajistar ADC, da wasu jam'iyyu hudu saboda rashin cika sharudda
  • Kotun ta ce jam’iyyun da aka ce a soke rajistar su sun gaza samun kaso 25% na kuri’u kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada
  • Masana na ganin hukuncin kotun na iya shafar takarar Atiku Abubakar da wasu ‘yan siyasa kafin zaben shekarar 2027 a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyun siyasa hudu.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin, inda ya ce jam’iyyun sun gaza cika sharuddan da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada domin ci gaba da kasancewa a matsayin halastattun jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

"Muna kira ga fannin shari'a"; Atiku ya dauki zafi kan umarnin kotu na soke rajistar ADC

Kotu ta ba INEC umarnin a soke rajistar jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyu 4.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Ojo Amupitan (hagu) da Tutar jam'iyyar ADC (dama). Hoto: @inecnigeria, @ADCNig
Source: Twitter

An hana jam’iyyu 5 shiga zabukan 2027

Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun hada da ADC, Accord (A), AA, APP da ZLP, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kotun ta ce jam’iyyun sun gaza samun akalla kaso 25 cikin 100 na kuri’un da ake bukata a zabukan baya, kamar yadda doka ta tanada.

Mai shari’a Lifu ya kuma umarci INEC kada ta bari jam’iyyun su shiga zabuka masu zuwa, ciki har da babban zaben shekarar 2027.

Kafin yanke hukuncin, kotun ta yi watsi da korafe-korafe da bukatun farko da wadanda ake kara suka gabatar.

Karar da aka shigar don soke rajistar

Wata kungiyar da ke dauke da sunan "Tawagar amintattu ta kungiyar tsofaffin 'yan majalisu ta kasa" ce ta shigar da karar.

Kungiyar ta hada da babban lauyan gwamnatin tarayya a karar tare da sanya INEC a matsayin wanda ake kara na farko.

Masu karar sun kafa hujja da cewa jam’iyyun da abin ya shafa sun kasa cika sharuddan da suka shafi yawan kuri’u da kuma tasirin siyasa a fadin kasa.

Kara karanta wannan

1959 zuwa 2026: Lokuta 5 da Hausawa da Ibo suka haɗu a siyasance kafin tafiyar OK a NDC

Sun bukaci kotu ta soke rajistar jam’iyyun saboda gazawarsu wajen cimma bukatun da kundin tsarin mulki ya tanada.

Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci cewa jam'iyyun sun gaza cika sharuddan zama jam'iyyu a Najeriya.
Harabar babbar kotun tarayya Abuja. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Hukuncin na iya girgiza siyasar Najeriya

Masana na ganin cewa hukuncin kotun na iya yin tasiri sosai ga zabukan da ke tafe, musamman babban zaben shekarar 2027 da kuma zabukan gwamnoni a jihohin Ekiti da Osun.

Idan aka fara aiwatar da hukuncin nan take, hakan na iya hana ‘yan takarar jam’iyyun shiga zabukan da ke gaba, a cewar rahoton Premium Times.

Cikin fitattun ‘yan siyasar da hukuncin zai iya shafa akwai Atiku Abubakar wanda kwanan nan ya zama dan takarar shugaban kasa na ADC.

Haka kuma, Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, na daga cikin wadanda hukuncin zai iya shafa yayin da yake neman wa’adi na biyu karkashin jam’iyyar Accord.

Kotu ta yi hukuncin kan rikicin shugabancin ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Kotun Koli ta tabbatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark a matsayin shugaban ADC na kasa.

Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Mohammed Lawal Garba ya soke umarnin kotun daukaka kara na a tsaya inda ake.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi maraba da wannan hukunci, yana mai cewa akwai sauran aiki a gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com